Sakataren Gwamnatin Katsina Ya Wakilci Gwamna Radda Wajen Kaddamar da Littafi Kan Kalubalen Mulki da Tsaro
- Katsina City News
- 29 Dec, 2024
- 133
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wani babban taro da aka gudanar a Hill Site Hotel, Katsina, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, wajen kaddamar da wani littafi da ya yi bayani kan kalubalen mulki da tsaro a Najeriya. Taron, wanda aka shirya domin tunawa da cikar shekaru biyu na naɗin Sardaunan Katsina, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, ya samu halartar fitattun mutane daga bangarorin ilimi, gwamnati, da kuma Sarakunan gargajiya.
Littafin, mai taken "Traditional Institutions and the Challenges of Governance and Security in Contemporary Nigeria," wanda ya tattaro kasidu (Lectures) na fitattun masana da suka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba 2023 na bikin cikar shekara daya da nadin Ambassador Ahamed Rufa'i Abubakar a matsayin Sardaunan Katsina. Mayan baki da suka samu halartar gagarumin Taron sun hada da Farfesa Attahiru Jega, CFR, da ya samu wakilci, da Farfesa M.D. Suleiman. Ambasada Farfesa Tijjani Muhammadu-Bande, GCON, Baraden Besse, shi ne ya jagoranci taron kaddamarwar tare da gabatar da jawabin bude taro.
Babban jawabi mai taken "Politics and Religion in Northern Nigeria: The Ulama in a Changing Political Landscape," ya samu gabatarwa daga Farfesa Muhammad Sani Umar, wani shahararren masani a bangaren tarihi. Jawabin ya yi tsokaci kan rawar da malamai ke takawa a siyasa da cigaban al’umma.
Masu sharhi irinsu Farfesa Yusuf Abdullahi daga Jami’ar Jos da Farfesa Mansur Ibrahim Mukhtar daga Northwest University, Kano, sun bada gudunmawarsu wajen tattaunawa, inda suka kawo hangen nesan masana daga fannoni daban-daban.
A jawabin nasa, Farfesa Shehu Salisu Muhammad, Mataimakin Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU), ya jaddada mahimmancin hada al’adun gargajiya da tsarin mulkin zamani. Har ila yau, an fara taron da addu’o’in musamman daga Alhaji Khalilu Musa Kofar-Bai, sannan aka rufe da addu’ar Mallam Ahmad Bello Wali, wanda yaba da godewa wadanda suka shirya taron gami da takaitacciyar tunatarwa.
An karkare taron da godiya daga Hon. Injiniya Bala Almu Banye, FNSE, Zarman Katsina, wanda ya gode wa dukkan mahalarta da wadanda suka taimaka wajen ganin taron ya samu nasara.
Wannan taro ya zama wata dama ta karrama gudunmawar ilimi tare da jaddada bukatar samun hanyoyin magance matsalolin da ke addabar tsarin mulki da tsaro a Najeriyar yanzu