NAHCON ta amince da kamfanoni 10 don jigilar aikin Hajjin 2025

top-news

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta zaɓi kamfanoni masu zaman kansu da ke jigilar aikin Hajji da Umrah guda 10 da za su yi jigilar alhazai s Hajjin 2025.

A cewar Hukumar, sauran kamfanoni 108 da ta tantace za su haɗu don ƙirƙirar ƙungiya ƙarƙashin waɗannan kamfanoni 10, bisa ga sabon tsarin da Saudiyya ta gabatar, wanda ke mai da hankali ga sauƙaƙe tsarin gudanar da ayyukan hajji.

Ga jerin kamfanonin da aka amince da su:

SHIYYAR ABUJA

Alkhauthar Travel and Tour Ltd

Omosa Travels Limited

Portfolio Travels and Tour Limited

SHIYYAR KANO

Arafat Air Services Nigeria Limited

Dala Air Services Limited

Hamsyl Travels and Tours Limited

Zango Travels and Tours Limited

SHIYYAR LAGOS

Al Hujaaj International Umrah and Hajj Services

Habdat Xpress Travels

Shebra Travels Limited