Gwamnatin jihar Katsina ta Dauki Matasa 369 Don Gudanar Da Aiki A Hukumar Hisbah

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Gwamnatin jihar Katsina Ta Dauki Matasa 369 tare da basu Horo Don gudanar da Aikin Hisbah a jihar Katsina.

Matasan da aka dauka daga Kananan Hukumomi 34 na jihar Katsina sun fara samun horo a karkashin kulawar hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defiance dake kan titin Batsari a garin Katsina.

Babban Kwamandan Hukumar Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) ya ziyarci sansanin don ganin yadda aikin bada horon ke gudana, gami da yin nasiha ga matasan maza da mata da suka hada bangarorin Addini na Darika, Izala, Shi'a da Kur'aniyyun.

Dakta Abu Ammar ya ja hankalin su akan tsoron Allah, gaskiya da nuna 'yan'uwanta ta Musulunci. Yace "Dukkanin ku ku Dakarun Musulunci ne, zakuyi alfahari da cewa kune Dakarun Hisbah na farko da aka kafa don kauda barna a fadin jihar Katsina, a cikin ku akwai dan Izala, Darika, Shi'a Dmda Kur'aniyyun amma dukkm cikarku nan aikin Allah ya hada mu, don haka muyi gaskiya muyi don Allah, saboda dama can aikin agaji ana koyar da aiki don Allah ne, sana kuma ita hukumar Hisbah tazo ne don aiki na cika umarnin Allah, (Amru Bil'marufi Wayan'hauna Alal Munkar) inji shi.

A bayan Doguwar Nasiha da jan hankali Dakta da tawagar da suka rufa masa baya, sun zagaya ko una a sansanin don ganin komi na tafiya lafiya.

Horon da aka fara daga ranar Litinin zai kwashi kimanin kwanakin goma sha hudu don tabbatar da kowannen su ya fahimci abinda aka daukeshi don shi.