An Zargi Jirgin Sojin Nijeriya Da Kuskuren Kai Hari A Wasu Kauyuka A Sokoto.
- Katsina City News
- 25 Dec, 2024
- 112
Wasu rahotanni daga jihar Sakkwaton Nijeriya na shigo wa Jaridar Taskar Labarai cewar, mutane da dama ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon kuskuren harin da jirgin yakin sojin Nijeriya ya yi na jefa Bama-bamai a kyauyukan Sidan Sama da Rumtumawa a cikin karamar hukumar Silame ta jihar Sakkwato.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 7:00 na Safiyar ranar Larabar nan, 25 ga Disamban 2024.
Wasu labarai sun bayyana cewar, kuskuren jefa Bama-baman da jirgin ya yi, ya faru ne a kokarin da jirgin ke yi na kai hari a wata tungar Lakurawa da 'Yanta'adda da ke makwabtaka da kauyen, inda tsautsayin hakan ya faru ga kyauyukan da ba su ji ba su gani ba.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa majiyarmu cewar, kauyukan biyu da harin ya shafa suna kusa da dajin Surame wanda ya zama mafakar ‘yanta’addan Lakurawa da ‘yanbindiga.
Majiyar, ta labarta mana cewar fiye da mutane 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon harin.
Shugaban karamar hukumar Silame, Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce suna ci gaba da tantance barnar da harin ya yi wa al'ummomin nasu, RFI Hausa ta ruwaito.
"Al'ummar ƙauyukan na zaune lami lafiya lokacin da jirgin yakin ya yi ruwan wuta kan jama'a.
Ya yi wuri na tabbatar da adadin mutanen da harin ya kashe ko suka samu raunuka saboda har yanzu muna tattara bayanai." In ji shi
Sai dai ya zuwa hada wannan rahoton, hukumar Sojin Nijeriya ba ta magantu kan lamarin ba tukunna.
In dai ba a manta ba, a watan Disamban shekarar 2023 ne al'ummar Tudun Biri da ke yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, Ibtila'in kuskuren harin jirgin soji marar matuki ya shafe su, a yayin da suke taron Mauludi, inda mutane sama da 100 suka riga mu gidan gaskiya wasu da dama suka samu raunuka.
Hoto: BBC Hausa