Kungiyar Muryar Talaka Ta Shirya Taron Tunawa Da Shehu Musa 'Yaradua A Katsina.
- Katsina City News
- 24 Dec, 2024
- 117
Auwal Isah Musa (Katsina Times)
Kungiyar nan mai rajin wayar da kan Talaka ta kasa reshen jihar Katsina, Murayar Talaka, ta shirya taron tunawa da Janar Shehu Musa 'yar'adua Katsina.
Taron mai taken "Tunawa Da Janar Shehu Musa 'Yar'adua" wanda ya samu halartar masana tarihin Marigayin da wasu ba'alin kungiyoyin al'umma, ya gudana ne a ranar Talatar nan a dakin taro na cibiyar koyar da Sana'o'i da Dogaro Da Kai 'Katsina Vocational Training Centre (KVC)' da ke Dutsin Amare Katsina.
An gabatar da maudu'ai daban daban da suka danganci, rayuwarsa, karatunsa, aikinsa, gwagwarmayar siyarsa, mukamai irin abubuwan ci gaban al'umar arewa da kasa baki daya da ya kafa.
Jawaban da aka gabatar a taron, masana sun bayyana Shehu musa a matsayin mara tsoro, dan fafutikar tabbatar da Dimukradiyya, kuma mai kishin al'ummar arewa na gaskiya, sannan abin koyi duk dan kasa nagari.
Maudu'an da aka gabatar a wajen sun hada da: "Tarihin Rayuwar Shehu Musa", "Janar Shehu Musa da gwagwarmayarsa ta tattabar da Dimukradiyya a Nijeriya", da kuma "Darussan da matasa masu tasowa za su koya daga Shehu Musa 'yar'adu".
"Shehu Musa shi ya tsaya tsayin daka jam'iyyar NPN ta tsayu, kuma shi ya jajirce aka tsaida Shagari dan takarar shugaban kasa har ya ci zabe a karkashinta a maimaikon Awolowo saboda kishin arewa." -Malam Sabo Musa a jawabinsa a taron
Duk a cikin jawabin nasa, Malam Sabo Musa ya kuma bada shawara da cewar, "Duk yaron da ya shiga Firamare, ya kamata a ce ya samu tarihinsa domin ya san irin gudummuwar da ya bayar a kasar nan." -In ji shi
Wadanda suka halarci taron da gabatar da jawabi a wajen sun hada da: Mai ba gwamna shawara kan wayar da kan al'umma Malam Sabo Musa, Danmajalissa mai wakiltar Charanci/Batagarawa Honorabul Usman Murtala Banye wanda ya samu wakilcin Dr. Muhammad Haruna Tsagero, Shugaban kungiyar 'Yanjarida ta kasa reshen jihar Katsina(NUJ) Kwamared Tukur Hasan Dan Ali, Shugaban Kamfanin buga Jaridu na Matasa MediaLinks Alhaji Danjuma Katsina da sauransu.
Daga bisani kuma, an ba da dama ga mahalarci domin yin tsokaci da shawarwari a taron.
Marigayi shehu Musa 'Yar'adua, ya rasu a ranar 8 ga Disamban shekarar 1997 a kurkukun Abakalike, lokacin mulkin Soji na Janar Sani Abacha.