Hukumar FIRS ta Buɗe Ƙofar Neman Ma’aikata Masu Ƙwarewa a Harkar Haraji, ICT da Wasu Sassa

top-news

Hukumar Federal Inland Revenue Service (FIRS) ta sanar da fara tantancewa da ɗaukar ma’aikata masu ƙwarewa domin cike muhimman gurabe a sassa daban-daban na hukumar.  

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an bayyana guraben aiki a fannoni kamar binciken haraji, ayyukan shari’a, hulɗa da jama’a, ICT, da kuma tsaro ta hanyar sadarwa (cybersecurity).  

A cewar hukumar, wannan shiri na ɗaukar ma’aikata ya yi daidai da manufofinta na ƙarfafa gwiwar ma’aikata da inganta ayyukanta don samun nasarori masu ɗorewa.  

Sharuɗɗan Cancanta
Sanarwar ta bayyana cewa masu neman guraben dole ne su kasance suna da digiri na farko ko kuma Higher National Diploma (HND) tare da matsayi na aƙalla Second-Class Lower Division ko Lower Credit. 

Haka zalika, dole ne masu neman aikin su kasance sun kammala National Youth Service Corps (NYSC) kafin ko zuwa ranar 31 ga Disamba, 2017.  

An kuma ƙara da cewa, masu neman matsayin Assistant Manager da Deputy Manager dole ne shekarunsu bai wuce 40 ba, yayin da waɗanda ke neman matsayin Senior Manager da Assistant Director dole su kasance ƙasa da shekara 45 a ranar 31 ga Disamba, 2024.  

Guraben Aiki da Matsayi
Guraben sun haɗa da mukamai guda 14, kamar Assistant Manager (Tax Investigation), Deputy Manager (Legal), da Assistant Manager (ICT), tare da albashin da yake kan mataki daga 04 zuwa 08.  

Hukumar ta nemi waɗanda ke sha’awar guraben su nuna ƙwarewa a bincike, hulɗa, jagoranci, da kuma fahimta mai zurfi game da dokokin haraji na Najeriya da tsarin mulkin hukumar.  

Hanyar Neman Aikin
Masu sha’awar neman aikin an umurce su da su cike takardun neman aiki ta hanyar shiga shafin tantancewa na FIRS ko kuma ta hanyoyin sadarwa na hukuma da aka tabbatar. Za a fara karɓar buƙatun neman aiki daga ranar Litinin, 23 ga Disamba, 2024, kuma za a rufe ranar 11 ga Janairu, 2025.  

Hukumar ta FIRS ta ƙarfafa waɗanda suka cancanta da su yi amfani da wannan dama don bada gudunmawarsu ga cigaban ƙasa. Haka kuma, hukumar ta tabbatar da cewa za ta gudanar da tantancewar cikin gaskiya da adalci.