Wata Miyar Sai A Makwafta: Gwamnatin Legas Ta Bada Kyauta Ga Ma'aikata Saboda Sabuwar Shekara Da Kirsimeti
- Katsina City News
- 21 Dec, 2024
- 206
Gwamnatin Jihar Legas ta amince da biyan albashi na 13 (na wata daya gaba ɗaya) ga dukkan ma’aikatan gwamnati na jihar, ciki har da ma’aikatan kananan hukumomi, hukumar LASUBEB, da kuma tawagar Neighborhood Safety Corps. Wannan biyan albashi na musamman ya kasance wata kyauta da gwamnati ta tanada domin rage wa ma’aikata wahalar hauhawar farashin kayayyaki, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
A cewar sanarwar da Ofishin Shugaban Ma’aikata ya fitar a ranar 17 ga Disamba, 2024, kashi 50% na wannan kyauta za a biya shi tare da albashin watan Disamba 2024, yayin da sauran rabin za a biya shi tare da albashin watan Janairu 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan matakin ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da walwala da jin daɗin ma’aikatanta, tare da ƙarfafa musu gwiwa domin ci gaba da bayar da gudummawa wajen cimma manufofin cigaban jihar.
An bukaci dukkan shugabannin ma’aikatu, hukumomi da sassa (MDAs) su sanar da ma’aikatansu wannan cigaba, tare da tabbatar da ganin cewa ya samu karɓuwa a dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
Gwamnatin Legas ta bayyana cewa wannan kyauta ba wai kawai rage wahalar rayuwa za ta yi ba, har ma tana da nufin zama wata hanya ta nuna godiya ga ma’aikata saboda jajircewarsu da sadaukar da kansu wajen inganta ayyukan gwamnati.