NNPC Ta Musanta Rahoton Da ke Cewa Matatar Man Port Harcourt Tsaya
- Katsina City News
- 21 Dec, 2024
- 207
Katsina Times
Hukumar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC Ltd) ta musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada, cewa tsohuwar matatar Port Harcourt da aka sake farfado da ita watanni biyu da suka gabata, ta daina aiki.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa wannan labari ba gaskiya ba ne, domin kuwa matatar tana aiki yadda ya kamata kamar yadda tsoffin shugabannin NNPC suka tabbatar bayan duba ta kwanan nan.
Sanarwar ta ce, "A halin yanzu, ana ci gaba da shirye-shiryen aikin lodin kaya na yau." Hukumar ta yi kira ga al'umma da su yi watsi da irin wadannan rahotanni marasa tushe, da ta ce sun samo asali ne daga masu neman haddasa karancin mai domin amfanin kansu.
NNPC ta tabbatar da cewa tana jajircewa wajen tabbatar da isar man fetur ga 'yan Najeriya ba tare da wata matsala ba.