Nasarorin Tinubu” Da Kuma Zahirin Halin Da Mutanenmu Suke Ciki A Kullum
- Katsina City News
- 19 Dec, 2024
- 184
Farfesa Usman Yusuf
Talata 18, Disamba 2024
A ranar 13 ga watan Nuwambar 2024, `yan Nijeriya suka gamu da bahallatsar, da ba ta kamata a ce ta fito ne daga Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Akan Tsaro (NSA) Mallam Nuhu Ribadu ba, a lokacin da ya wakilci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron Babban Shugaban Hukumar Kwastam a Abuja. Ya yi magana a kan tsaron kasa, da tattalin arziki da kuma halin da kasa take ciki.
Yana ta fankama da bandan-bandan da jibin goshi wajen ganin ya sauya taken bakar wahalar Tinubu da ake yi wa lakabi da T-Pains, ya ba shi sabon taken “Tinubu Gains” wato Nasarorin Tinubu.” - NSA
A lokacin da yake ta kidansa yana rawarsa da zakewa wajen yabon `Mai Gidansa da ludayinsa yake kan dawo’, mutum zai iya gani baro-baro kunci da rudewar gwamnatin da ba ta san halin da `yan kasa suke ciki ba, duk da tarin ayarin masu ba da shawara bangaren kafofin yada labaru har su 13, da makadan yabo, da `yan wasa, da malaman addini, da masu neman aiki ruwa a jallo suka yi cincirindo domin tallata tsare-tsaren ta na tattalin arziki da suka zamewa jama`a jafa`i.
Abu muhimmi, an yi jawabin ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu take ta tsilla-tsilla, ga matsalar tsaro, da rashin hakurin jure wa `yancin da `yan kasa suke da shi na sukar ta. Ga dai abin da Mai Ba Shugaban kasa Shawara Akan Tsaron ke cewa a game da batutuwan da ke biye.
A Game Da `Yan Fashin Daji:
“A kullum ana kashe daruruwan `yan fashin daji, da dama suna mika wuya ko ranta wa na kare, wannan Nasarorin Tinubu ne. Sassan kasarmu da dama ana zaune lafiya a yau. Wannan Nasarar Tinubu ne.” - NSA
Shin tsaro yana inganta ne a Arewa maso yamma da Arewa Maso Tsakiya kamar yadda Mai Ba Da Shawarar yake so mu yarda? A yanzu haka da muke wannan maganar, mutanenmu da dama da suke yankunan karkara ba sa iya kwana a gidajensu, dubbansu suna daji hannun `yan fashin daji, sannan manoma ba su iya zuwa gonakinsu.
Manyan titunan tarayya kamar su hanyar Funtua zuwa Gusau da ke jihar Zamfara, da Katsina zuwa Kankara ta jihar Katsina sun zama tarkon mutuwa, inda `yan fashin daji suke cin karensu babu babbaka, su tare hanya, su jidi fasinjoji son ran su.
Mai Ba Da Shawarar Bangaren Tsaron ya ce karon farko a Nijeriya hukumomin tsaro sun hada kai suna aiki tare a matsayin tsintsiya daya madaurinki guda. Abin da ake sa rai da haka, shi ne a gani a kas wajen kyautata tsaro, an ce da kare ana biki a gidanku, ya ce in gani a kas. Sai dai a zahiri ba a gani a kas ba.
Rahoton tsaro a Nijeriya na watan Oktoban 2024 da kamfanin Beacon Security and Intelligence Ltd, kamfanin da ke kan gaba wajen lamuran tsaro a Nijeriya ya fitar, yana nuna cewa a watan Oktoba na 2024, wata ne da aka fi fama da barna da kashe karshen al’umma har guda 1,545 (karuwa kashi 51 cikin kashi 100 idan aka kwatanta da watan Satumba na 1022) kuma satar jama`a mafi yawa ta 971 (karuwar kashi 24.42 daga 807 da aka yi watan Satumba). Jimillar wadanda aka kashe daga watan Janairu zuwa Oktoba a shekarar 2024 su ne mutum 12,000, adadin da rabon da a ga irinsa tun shekarar 2013 da aka yi fama da Boko Haram da aka ce ita ce kungiya mafi hadari a duniya.
Jimillar wadanda suka rasa rayunkan su daga Janairu zuwa Oktoba sun kai 13,545. Watau shekarar 2024 ta kasance mafi muni cikin shekaru goma da suka gabata.
Bangaren dalilan kuwa shi ne saboda yawan dogaro da amfani da karfin bindiga, da ke zama abin daukar aiki maimakon mayar da hankali ga musabbabin matsalar. Sauran muhimman bangarorin a yaki da `yan fashin dajin kamar wadata bangaren `yan sanda, da tattara bayanai na sirri, da rage tsadar rayuwam da batutuwa na muhalli da yanayi, duka an yi watsi da su.
Har yanzu kalaman da Albert Einstein ya yi gaskiya ne da yake cewa “Babu yadda za a yi a wanzar da zaman lafiya ta amfani da karfi; za a iya cimma hakan ne ta hanyar fahimta.”
A Game Da Boko Haram (BH)
“Boko Haram, da ta addabi kasarmu, a yanzu suna ta gudu. `yan kungiyar a yanzu haka suna ta gudu kasashen makwabta saboda Nijeriya ta musu zafin da ba sa iya ci gaba da kai hare-haren su.” - NSA
Bayan tserewa zuwa kasashe makwabta, mayakan Boko Haram sun mayar da hare-harensu zuwa yamma, zuwa Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Tsakiya, inda suke hada mummunan kawance da `yan fashin daji, suna koya musu yadda ake hada bama-bamai da yadda ake amfani da su. Mun ga wasu daga cikin sakamakon wannan mummunan kawance a mugun harin da aka kai a jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2021, da fasa Gidan Gyara Hali na Kuje a ranar 4 ga watan Yulin 2021.
A gidanta da ta yi kaka-gida da ke Arewa maso gabas, Boko Haram ta ci gaba da zama babbar barazana saboda sake bullar amfani da abubuwa masu fashewa da `yan kunar bakin wake.
A Game Da Lakurawa: “Wadanda ake kiran su da Lakurawa ko me ma suke kiran kan su da shi suna kuskure ne, za a gama da ku, kuma za mu kore ku daga Nijeriya.” - NSA
Sabanin abin da Manjo Janar Edward Buba, Daraktan, Yada Labaru na Aikace-Aikace Tsaro, da ya yi bayani a daya daga cikin ganawarsa da manema labaru, cewa kungiyar sabuwa ce a Nijeriya, a yanzu mun san cewa kungiyar tana nan tun 2017, lokacin da al`umomin karkara suka gayyato su, su taimake su yaki da `yan fashin daji. Wannan bakuwar gayyata ta auku ne a idon gwamnatocin jihohi da ta tarayya da dukkan hukumomin tsaro.
Abin bakin ciki shi ne an gayyato `yan ta`adda na kasashen waje zuwa cikin gida Nijeriya, kasa mai `yancin kanta, domin gudanar da aikin hukumominmu na tsaro.
Ainihin tambayoyin da ya kamata `yan Nijeriya su yi su ne: me ya sa sojoji a yanzu suke nuna ba su da masaniya a game da wannan kungiyar `yan ta`adda da ta shekara bakwai tana Nijeriya kuma me ya sa aikace-aikacenta suka fi kamari a yanzu?
Abin kyamar da wadannan kungiyoyi na `yan ta`adda suke aikatawa a kullum a kan mutanenmu, abubuwa ne na zahiri kuma kusa da mu da muka fito daga jihohin sassan Arewa maso yamma da Arewa Maso Tsakiya. Tabbas abu ne da ya shafe ni, ni kashin kaina a matsayina na wanda ya fito daga jihar Katsina, inda kashi 65 cikin 100 na jihar `yan fashin daji sun addabe shi.
Saboda haka muke ganin ana wasa da hankalinmu ne da rena mana wayau idan muka ji Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Akan Tsaro yana yawan maimaita wannan farfaganda, da rabin gaskiya a game da matsalar tsaro a jihohinmu.
A lokacin da `yan kasa suke fama da matsalar tsaro da bakar wahala sakamakon karuwar tsadar rayuwa da yunwa, abin da `yan kasa suke so su ji daga shugabannin su shi ne kalamai masu dadi na tausayawa da lallashi, ba kalamai irin na marasa imani da tinkaho ba, da ke nuna ba a ma san wahalhalun da jama`a suke ciki a kullum ba.
Maido da gyarawa da huldar diflomasiyya da kasashen Nijar, da Burkina Faso, da Mali na da muhimmanci domin zaman lafiyarmu da tsaro. Kawo sojoji na kasashen ketare a jibge su a Nijeriya, ko ma da me aka fake don kawo su, zai kara sa barazanar tsaro daga `Yan fashin daji, da Boko Haram, da ISWAP, da Lakurawa da sauran kungiyoyin ta`adda da dama ta kara tabarbarewa.
A Game Da Neja Delta:
“Je ka Neja Delta, hankali ya kwanta, A yanzu haka Nijeriya tana hako da ganga milliyan 1.8 ta danyen mai a kowacce rana, adadin da aka dade ba a samu ba, Nasara ce ta Tinubu.” - NSA
Mai Ba Da Shawarar Bangaren Tsaro cikin dabara ya ki cewa uffan a kan satar mai da badakalarsa. `Yan Nijeriya suna so su san me ake yi domin dakatar da masu satar mai, da kama su da kuma hukunta su.
Batun Tattalin Arziki:
“A yau an tsabtace Babban Bankin Nijeriya ba kamar shekarar 2023 ba, wannan Nasara ta Tinubu ce.” Naira za ta kwatar wa kanta `yanci ku jira ku gani. Hukumar Kwastam ta Nijeriya karon farko ta tara Naira Tiriliyan 5, wannan Nasara ta Tinubu ce.” - NSA
Duk wadannan alkalumma tamkar babu su ne samsam ga `yan kasa saboda ba su yi wani tasiri wajen kawo sauki, daga karuwar tsadar rayuwa da suke fama da ita ba. Tsare-Tsare na tattalin arziki na Shugaba Tinubu sun jefa karin miliyoyin `yan Nijeriya cikin miliyan 133 da ake da su, da suke ta fama da fatara iri-iri.
Maimakon rage makudan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da mulki, da rage haraji, da ba da tallafi na gaskiya ga `yan kasa da suke fuskantar matsananciyar wahala a rayuwarsu, gwamnatin Shugaba Tinubu ta ci gaba da dora wa `yan kasa da kamfanoni harajin da ya gagare su biya.
Manya manyan kamfanonin duniya guda biyar ne su ka fice daga kasar nan a 2024 saboda yanayin da ya musu tsauri wajen gudanar da kasuwancinsu.
Masu ruwa da tsaki daga dukkan sassan kasar nan sun nuna rashin amincewarsu da kudirin dokar sabon haraji da Shugaban Kasa Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Kasa, saboda harajin zai fi ba da fifikon raya tattalin arzikin jihohin Legas, da Ogun da Ribas, da danne sauran jihohin kasar nan 33, amma Shugaba Tinubu ya yi kememe, ya yi kunnen-uwar-shegu da korafe-korafen da ake ta yi a kai, ya nace sai majalisa ta amince da kudirin ya zama doka.
Ba ni da wani shakku ko tababar cewa an shirya wannan hayagagar ce a kan kudirin harajin domin karkatar da hankalin `yan kasa daga bakar wahalar da tsare-tsaren tattalin arziki na gwamnati suka jefa su a ciki.
Tsarin shugabanci na Tinubu da ke cike da dagawa, da rashin tintiba a kan muhimman matakai na tsare-tsare kamar su cire tallafin mai, da karya darajar Naira, da karkata bangare guda a nade-nade na mukaman hukumomin tarayya, da kudirin dokar haraji, da kuma rungumar kasar Faransa da ya yi, sun kara fadin gibin da ke tsakanin gwamnati da `yan kasa, kuma ya yi mummunar raba kasar.
Ga masu sukar gwamnati: “ Wannan Nijeriya ce ta 2024, zan iya ba ku tabbacin cewa masu sukar za su yi shiru daya bayan daya. Ga masu suka, za mu rufe muku baki, za mu yi hakan.”
Rashin jurewar Shugaba Tinubu a bincike gwamnatinsa abin fahimta ne saboda shekara 25 da ya yi yana mulkin Legas a matsayin wata Daula da babu wani dan jihar da ya nuna masa yatsa, kuma ya dauka hakan za ta kasance a wannan babban matsayi.
Mu muna sukar wannan gwamnati da tsare-tsarenta ne saboda hakkinmu ne a matsayinmu na `yan kasa a tsari na dimukradiyya saboda muna kaunar wannan kasa da muke kira tamu.
A kalaman Mark Twain, “Biyayya ga kasa a kowanne lokaci. Biyayya ga gwamnati idan ta cancanci ayi mata biyayya.”
A Game Da Shugaba Tinubu:
“Babu wanda ya taba yin fito na fito da Tinubu kuma ya samu nasara, babu shi. Babu wanda ya taba samun nasara a kan Tinubu. Tinubu nasara ne, bai taba gazawa ba.” - NSA
Mai Ba Da Shawarar Bangaren Tsaron ba ya bukatar a tunatar da shi cewa addinin Musulunci ba ya son ana koda dan Adam, komai girman matsayinsa, kuma kai mutum zuwa matsayin Ubangiji na daya daga cikin manyan zunubai ko shirka a Musulunci.
A Game Da Dangantaka Da Kasashen Duniya:
“A yau duk duniya tana kallon Shugaba Tinubu, Firaministan Indiya, da Shugaban Jamus zasu ziyarci Nijeriya, kuma an gayyaci Nijeriya ta halarci taron G-20. Fiye da gayyata 20 ga Shugaba Tinubu ya ziyarce su, wannan Nasarar Tinubu ce.” - NSA
Ya kamata yadda Shugaba Tinubu ya rungumi kasar Faransa da Firaministanta Emmanuel Macron, ya damu kowanne dan Nijeriya. A daidai lokacin da kusan duka kasashen da Faransa ta raina da ke Yammacin Afirka (Mali, da Nijar da Chadi, da Burkina Faso da Senegal) suke ta yanke wata hulda ta soja da Faransa, Shugaba Tinubu yana jan Nijeriya zuwa hannun Faransa ba tare da ya tuntubi kowa ba.
Daga tarihinta a Afirka, Faransa ba ta da wani abu da za ta ba Nijeriya in ba tabarbarewar tsaro da dibar albarkatun kasar mu ba.
Burin Faransa a Nijeriya shi ne samun damar hakar dinbin albarkatu na ma`adinai da ake da su a yawancin jihohin Arewacin Nijeriya, da amfani da damarmaki na hako mai da gas, da kafa sansani na soja domin maye gurbin wadanda suka kore su daga kasashe 5 da aka ambata a sama.
`Yan Nijeriya za su yi matukar bijire wa duk wani yunkuri da Shugaba Tinubu zai yi, na ba da izinin kafa wani sansani na sojojin kasashen waje a Nijeriya ko dibar dinbin albarkatunmu ba tare da an bi ka`idar daya kamata a bi ba.
Babbar barazana ga dukkan wani tsaro na kasa ita ce yunwa; akwai bakar yunwa a kasa, da, kamar yadda wani rahoto na baya-bayan nan na Hukumar Lafiya ta Duniya ke nunawa, cewa yunwar za ta kara ta`azzara a watannin Nuwamba na 2024 zuwa Mayu na 2025. Tuni Medecins Sans Frontieres (MSF) ta ankara cewa akwai tsananin yunwa a Arewa Maso yamma, da kashi 30 cikin 100 na yaran da suke fama da tsananin yunwa, suna garuruwan Jibiya, da Mashi, da Mani da ke jihar Katsina.
Amsar Tinubu ga yunwar da ta yi kamari a tsakanin jama`armu ita ce raba shinkafa a matsayin tallafi da zuwa yanzu sau tara (9) ana raba ta, babu wani sauki da aka samu.
Wani bayani na kwanan nan yana nuna cewa zuwa kashi 60 chikin dari na daliban da suke karatu a manyan makarantu da ke Arewacin Nijeriya, ba su iya komawa makarantun su ba, saboda karuwar tsadar rayuwa da kasa biya.
Hakazalika yawan yaran da basu zuwa makaranta yana ci gaba da karuwa tun daga lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki.
Jami`o`i suna ta kumajin an kara kudin lantarki, sai malaman jami`ai da suke ta yin tururuwa suna ficewa daga kasar nan babu kama hannun yaro. Duka wadannan suna da babbar illa ga tsaron kasa na Nijeriya.
Tsarin kula da lafiya na Nijeriya sai rushewa yake ci gaba da yi saboda yadda ma`aikatan lafiya suke ta gudu kasashen ketare, ga tsadar magani da ya sa mace-mace na karuwa saboda cutar da take da saukin warkarwa kamar su ciwon siga, da hawan jini, kuma asibiti suna ta kukan an kara musu kudin wutar lantarki da ya fi karfinsu.
Ba a taba gani a tarihin kasar nan cewa an jefa jihohi 17 cikin 36 na kasar nan (Dukkan su a Arewa) cikin duhu na tsawon kwana 14 ba, kamar yadda ya auku a ranar 29 ga watan Oktoba 2024. An danganta wannan daukewar wutar lantarki da aikin wasu `yan ta’adda da ya yi sanadiyyar asarar rayuka, musamman majinyata da suke asibitoci da kuma asarar hanyar samun abinci, inda aka tabka asarar tiriliyoyin Naira a tattalin arzikin yankin.
Wannan babban kisan-mummuke ne ga yankin da yake ta fama da matsalar tsaro, da bakar fatara, da yunwar da ba mu taba ganin irinta ba a rayuwarmu da Babban Bankin Duniya ya tsara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bi da tsarin tattalin arziki ya haifar.
A yanzu akwai wani babban abin damuwa da ke aukuwa a Arewa a lokacin mulkin Tinubu; muna ganin irin cin kashi da wulakanta sarakuna da gangan da ake yi a Arewa, kamar yadda muka gani a jihohin Kano, da Sakkwato, da Adamawa, da gwamnonin jiha suke da hannu dumu-dumu, suna taka rawar kidan da iyayen gidan su, suke kada musu.
Shawara ta tsakani da Allah ga Mai Ba Da Shawara Bangaren Tsaro ita ce ba yanzu ne lokacin yabon samun nasara ba; saukar da kai kasa, nesanci fitowa kana fankama, yi aiki tukuru baki alaikum, kauce wa aukawa ramin siyasa, fadada tintiba, ka san wahalhalun da jama`armu suke ciki tare da nuna tausayi a kalamanka da kuma a aikace. Ka tuna rantsuwar da ka yi da ka hau mukaminka, gobe Kiyama za a tsayar da kai ka fadi duka abubuwan da ka aikata a wannan muhimmin ofishin naka da ya shafi rayuwar miliyoyin `yan Nijeriya.
Muna Rokon Allah Ya Saukaka Mana Mu Duka.
Usman Yusuf Farfesa ne bangaren Nazarin Amosanin Jini Da Sauran Matsaloli na Jini da kuma Dashen Bargo.