KAMFANIN TURKIYYA YA FARA AIKIN INGANTA NOMAN ZAMANI A ZAMFARA YAYIN DA GWAMNA LAWAL YA KARƁI BAƘUNCIN RUKUNIN KAMFANIN DIREKCI
- Katsina City News
- 12 Dec, 2024
- 80
Wani fitaccen kamfanin ƙasar Turkiyya mai suna Direkci zai fara aikin samar da na'urorin zamani a harkar noma tare da samar da lambunan zamani domin bunƙasa noma a Jihar Zamfara.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Nurullah Mehmet, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na cibiyar Direkci, ya jagoranci tawagar da suka kai wa Gwamna Dauda Lawal ziyarar aiki a ofishinsa a gidan gwamnati da ke Gusau.
Kamfanin na ƙasar Turkiyya na shirin kawo sauyi a harkar noma a Jihar Zamfara ta hanyar noman auduga, da raƙe, da waken soya mai tarin yawa.
Baya ga noman gargajiya, cibiyar za ta bullo da hanyoyin noma na zamani, gami da amfani da fasaha wajen samar da lambuna da kiwon kaji, waɗanda za su ƙara inganta fannoni da dama a jihar.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da samar da abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar Jihar Zamfara.
“Kamar yadda na yi alƙawari a lokacin yaƙin neman zabe, idan aka zabe ni, gwamnatina za ta mai da hankali kan tsaro, noma da samar da abinci, ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki, da ƙarfafawa al'umma.
“An san al'ummarmu a jihar Zamfara da noma. Burin mu shi ne mu farfaɗo da wannan fanni. Muna da burin tabbatar da tsaron jihar domin mutane su koma gonakinsu.
“Abu mai muhimmanci shi ne, bayan tabbatar da tsaro a gonaki, mataki na gaba shi ne samar da na’urorin zamani ga manoman mu, kasancewar mun riga mun sami filaye da ma’aikata.
"Wannan shi ne dalilin da ya sa muke maraba da haɗin gwiwar masu zuba jari irin su Direkci.
“Na yi tafiya zuwa Turkiyya a watan Yuli, inda na ziyarci ayyukan gonaki, kiwo, ayyukan kiwon kaji, da kuma masana’antar sarrafa na'urorin ayyukan noma ta Turk. Cibiyar Direkci ta zo Zamfara ne domin bullo da ci gaban fasaha a harkar noma.”
A farko, Nurullah Mehmet, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Direkci, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara a cikin ƙanƙanin lokaci.
“Kamfanin mu Direkci yana gudanar da ayyuka da dama a jihohi daban-daban na Nijeriya.
“Shirin noma na Direkci a jihar Zamfara zai inganta darajar noma tare da jawo zuba jari, da bunƙasa tattalin arzikin cikin gida.
“Shigo da lambunan zamani zai habaka noma a duk shekara, wajen kare amfani gona daga fari da sauran abubuwa.
"Noman zamani da na kiwon kaji za su samar da guraben aikin yi a matakai daban-daban, daga ma'aikatan gona zuwa ƙwararru a harkar noma."