Nazari Kan Cin Zarafi A Nijeriya (2015-2024) Karuwa Ko Raguwa?
- Katsina City News
- 11 Dec, 2024
- 119
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Ranar 10 ga Disamba, Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana domin wayar da kai da kuma yin yaki da cin zarafi a duniya. Cin zarafi yana nufin keta hakkin bil'adama, wanda ya haɗa da amfani da karfi, cin fuska, ko keta doka, Addini da al'ada, wanda ke jefa mutane cikin halin kunci.
A Nijeriya, an samu rahotanni da dama akan cin zarafi daga jami'an tsaro da sauran sassa, musamman tsakanin shekarun 2015 zuwa 2024. Wannan nazarin zai duba ire-iren cin zarafi tare da misalan su da kuma yadda ya shafi rayuwar al’umma.
1. Cin Zarafi daga Jami'an Tsaro:
Wannan yana daga cikin manyan matsalolin da ke damun al'umma. Ana samun rahotanni da dama na cin zarafi daga sojoji, 'yan sanda, da sauran jami’an tsaro. Misalai sun haɗa da:
Zaria Massacre (2015): Inda ya ci gaba da zama darasi. Sojoji sun kashe daruruwan ‘yan Shi’a bayan rikicin da suka yi da kungiyar IMN (Islamic Movement in Nigeria).
Endsars (2020): Zanga-zangar matasa domin yaki da cin zarafi daga rundunar SARS (Special Anti-Robbery Squad) ta rikide zuwa gagarumar fitina. An samu rahotannin kashe-kashe da jikkata masu yawa a Lekki Toll Gate da wasu wurare.
2. Cin Zarafi a Lokacin Zanga-Zanga:
- End Bad Government Protest: Wannan ya ci gaba da nuna yadda gwamnati ke amfani da jami'an tsaro don dakile 'yancin fadin albarkacin baki, wanda ya kai ga harbe-harbe da cin zarafi a kan masu zanga-zanga, musamman a Kano da wasu jihohin Arewacin Nijeriya.
3. Cin Zarafi a Lokacin Ta'addanci da Rikice-Rikice:
- A lokuta da dama, jami’an tsaro suna amfani da karfin da ya wuce kima wajen yakar 'yan ta'adda da masu tada kayar baya. Misali, a yankin arewa maso gabas, rahotanni sun nuna yadda aka keta hakkin mata da yara yayin ayyukan sojoji.
4. Cin Zarafi daga Masu Mulki:
- Rahotanni da dama sun nuna yadda 'yan siyasa da masu rike da mukamai ke cin zarafin hakkokin jama'a ta hanyar amfani da jami'an tsaro ko tsare mutane ba bisa ka'ida ba.
Nazarin Matsalar (2015 -2024): Karuwa Ko Raguwa?
Bisa la'akari da rahotanni daga kungiyoyi masu zaman kansu, irin su Amnesty International, Human rights advocacy and awareness center IHRACC, da Human Rights Watch, cin zarafi a Nijeriya ya karu sosai tsakanin shekarun 2015 zuwa 2024. Hakan yana faruwa ne saboda ko inkula daga Gwamnati da kuma rashin hukunta masu laifi, rashin kyakkyawan shugabanci, da kuma tsauraran matakan da jami’an tsaro ke dauka.
Dalilan Karuwar Cin Zarafi:
1. Rashin Kulawa daga Gwamnati: Gwamnati ba ta daukar matakan ladabtarwa ga jami’an tsaro da ke keta dokoki.
2. Rashin Ingantaccen Tsari: Rashin isassun dokoki da tsare-tsaren da za su kare hakkin jama’a.
3. Rikice-rikice a kasar: Matsalolin tsaro kamar Boko Haram, IPOB, Barayi Masu garkuwa da Mutane (Bandits) da rikicin Fulani makiyaya sun sa jami'an tsaro sun fi amfani da karfi.
Misalan Cin Zarafi:
1. Rikicin Shi'a da Sojoji 2015 A Zaria an kashe farar hula fiye da dari uku, kamar yadda rahoton gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar.
2. Endsars (2020): Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutane sama da 56 a yayin zanga-zangar da ta shafi dukkan fadin kasar.
3. Cin Zarafi a Kaduna da Enugu: Rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya sun jawo kashe-kashe ba tare da daukar mataki ba.
4. Tsare-tsaren Rashin Adalci:Rahotanni daga Amnesty sun nuna yadda aka tsare mutane da dama ba tare da gurfanar da su a kotu ba.
Cin zarafi ya zama babban kalubale ga ci gaban Nijeriya. Don rage wannan matsala:
Ya kamata gwamnati ta kafa kwamitoci masu zaman kansu don binciken cin zarafi da hukunta masu laifi.
- A yi amfani da kayan zamani wajen sa ido kan jami'an tsaro.
- A wayar da kan jama’a kan hakkokinsu don kare kansu daga cin zarafi.
A takaice, cin zarafi ya karu sosai tsakanin shekarun 2015 zuwa 2024 saboda rashin kyakkyawan shugabanci da kuma tsauraran matakan da ake dauka kan masu fadin albarkacin baki. Wannan matsala tana bukatar matakan gaggawa domin kare hakkin jama'a da inganta zaman lafiya.