Dalilan da Suka Sanya Muka Nada Hamza Sule a Matsayin 'Sadaukin Kasar Hausa'
- Katsina City News
- 09 Dec, 2024
- 266
Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya ce masarautar tana bada sarautunta ne kadai ga mutanen da suka yi fice wajen yi ma alu’uma hidima.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin wata babbar tawaga da ta je fadarsa da ke Daura domin yi masa godiya bisa ba Alhaji Hamza Sule Faskari sarautar 'Sadaukin Kasar Hausa'.
Ya ce majalisar masarautar ta yi la'akari ne da dumbin aiyukan raya kasa da Alhaji Hamza Sule yayi lolacin da ya rike mukamin Kwamishinan Muhalli na Jihar.
Alhaji Umar Faruk Umar ya ce majalisar ta kuma yi la’akari da irin ayyukan da yake yi na taimakon mabukata, da gajiyayyu, da marayu da zawarawa, da gina rayuwar mata da matasa game da daukar nauyin karatun daruruwan dalibai da iyayensu basu da galihu.
“Lokacin da ya rike mukamin Kwamishinan Muhalli a jihar nan, kokarin da ya yi ya sa jihar ta samu damar cin gajiyar shirin Bankin Duniya na NEWMAP, kuma a karashin shirin an gudanar da manyan aiyuka a fadin jihar.
“Sun gina manyan magudanan ruwa wadanda suka taimaka wajen magance matsalar yawan afkuwar ambaliyar ruwa a jihar nan.
“Sun kuma aiwatar da ayyuka Masu yawa wajen kawar da zaizayar kasa a fadin jihar kuma hakan ya ceto kauyuka da garuruwa da gonaki da yawa daga zaizayewa.
“A nan Daura sun dasa itatuwa wadanda suka kawata mana kasarmu kuma suke kare mana kasa daga kwararowar hamada.
“Har ila yau muna sane da irin gagarumar gudunmawar da Alhaji Hamza Sule ya bayar wajen kyautata rayuwar mabukata, da matasa, da mata, da marayu, da 'yan gudun hijira da daliban da yake daukar nauyin karatunsu.
"Mun ba shi wannan sarautar ne don mu gode masa bisa waɗannan dumbin aiyuka na raya kasa da taimakon al'uma, muna fatan hakan zai kara masa kwarin gwiwa don ya ci gaba da irin wannan aiyukan,” inji Mai Martaba Sarkin na Daura.
Tawagar da ta raka Alhaji Hamza Sule a ziyarar godiyar ta hada da ‘yan majalisun jiha da na tarayya da kwamishinoni da manyan hakimai daga jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna, da shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da sauran jiga-jigan 'yan siyasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa.
Cikin tawagar har da dan majalisar wakilai mai wakiltar Malumfashi da Kafur, Alhaji Aminu Ibrahim, da tsohon dan majalisa mai wakiltar Faskari, Kankara da Sabuwa, Alhaji Murtala Isah Kankara.
Kauran Katsina Hakimin Rimi, shi ya jagoranci hakimai daga masarautar Katsina da Zazzau da Gusau da suka bi tawagar don bayyana godiya ga Sarki na Daura.