Najeriya Ta Sha Alwashin Cimma Manufar Samar da Gangar Mai Miliyan 2.06 a Rana
- Katsina City News
- 05 Dec, 2024
- 208
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Najeriya ta bayyana aniyarta na cimma burin samar da gangar mai miliyan 2.06 a rana yayin taron kungiyar OPEC karo na 38, wanda aka gudanar don nazarin ci gaban kasuwar mai a duniya.
Taron kwamitin sa ido na ministoci (JMMC) na kungiyar ƙasashen da ke fitar da mai (OPEC) ya gudana ranar Alhamis, inda sakamakon tattaunawar ya fito a wata sanarwa daga mai ba da shawara kan harkokin watsa labarai ga Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, wato Nneamaka Okafor.
Sanarwar ta bayyana cewa Ministan Lokpobiri ne ya jagoranci tawagar Najeriya a taron.
“Taron ya haɗa ministoci da shugabannin tawagogi don tattauna dabaru masu muhimmanci da nufin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a kasuwar mai ta duniya.”
Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin taron, mambobin OPEC da waɗanda ba mambobi ba sun jaddada biyayyarsu ga ƙa'idodin yarjejeniyar haɗin gwiwa (DoC) da aka kafa tun 2016, wanda aka ƙarfafa ta da sakewa a 2019 ta hanyar yarjejeniyar haɗin kai.”
“Wannan tsarin ya zama ginshiƙi a dabarun OPEC wajen kiyaye daidaito tsakanin samarwa da buƙatu a kasuwar duniya.”
Sanarwar ta kuma jaddada cewa an amince da tsare-tsaren da aka tsara a taron ministoci na 35 na OPEC, wanda zai ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen shekarar 2026. Hakan na da nufin tabbatar da cikakken bin dokoki da aiwatar da tsarin diyya don inganta gaskiya da kiyaye daidaito a kasuwa.
A cewar Lokpobiri, Najeriya na ganin wannan tsari a matsayin hanyar cimma burinta na samar da gangar mai miliyan 2.06 a rana kafin shekarar 2025, kamar yadda aka tsara a kasafin kudin 2025.
“Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan kokarin OPEC da haɗin kai tare da tsayawa tsayin daka wajen cimma burinta a fannin makamashi na duniya,” in ji Sanata Lokpobiri.
Gwamnatin Tarayya ta kuma jaddada kudirinta na inganta haɗin kai tsakanin ƙasashe mambobi na OPEC da sauran abokan huldar ƙasashen duniya don tabbatar da ci gaban makamashi mai dorewa.