IRE-IREN TAMBARI

top-news


Tambari guda goma sha biyu ne, idan aka aka haɗa harda Gwabron Tambari, kuma kowane da kalar amon sautin da yake fitarwa.

Shi Gwabron Tambari, na Sarkin Katsina Muhammadu Korau ne, shine ake buga ma sabon Sarkin Katsina idan aka naɗa shi, wanda Galadima ke buga wa sau Goma sha biyu, kuma shi Kumbo ne aka yi amfani da shi wajen haɗa da"ma'ana Tasa.

 *LANGARU* 

Akwai guda biyu wanda su kuma an yi su zamanin Sarkin Katsina Abubakar Saddiƙu, suma Kumbo ne aka yi amfani da shi wajen hada Tambarin.

Sauran kuma akwai waɗanda lokacin Dallazawa aka yi su wasu kuma an yi su zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko.

Shi langaru da shi ake fara tada kiɗin buga Tambari, saboda zaƙin yanda yake fitar da amon sautinsa, za'a ganshi ƙarami, kuma da shi ne ake canza kalar kiɗin tambari.

 *SAUYI*

Shi sauyi shi ne fitar da kiɗan langaru da shago/jifa ya haɗa su baki ɗaya, zai fidda salo salo na kiɗan.

 *SHAGO*

Shi kuma ana amfani da shi wajen yin jifa, domin fitar da amon sauti mai dogon zango, shiyasa za'a ganshi Babba, kuma yafi duk sauran tambarin fitar da amon sauti mai nisa, sannan idan kana kusa da shi ba lallai ne kaji ƙarar fitar sautin sa ba. Amma idan kana nesa zakaji yana Dum Dum Dum yana kai saƙon sa nesa ne.

Kuma shi mai buga shi yafi duk masu buga langaru da sauyi shan wahala, duba da yanayin yanda yake dukan shi da ƙarfin sa.

 *BABBAN AIKIN SARKIN TAMBURA*

1. Buga Gwabron Tambari idan an naɗa ɗaya daga cikin Hakiman Karaga.
2. Hawa tare da buga Tambari yayin bukin Hawan salla ko Durba wanda sarkin Katsina ya halarta.

3. Yin sati ɗaya yana buga Tambari a kofar gidan sarki a lokacin bukin salla.

4. Kaɗa Tambari a lokacin da sarkin Katsina ya yi tafiya ya dawo gida Katsina, da sauransu.

*KIRARIN TAMBARI*

1. In kaji Tambari Sai Sarki
2. Tambari ajika sama'u
3. Tambari Basarakiyar Ganga
4. Tambari Gangar Sarakuna
5. Tambari kiɗan da ba Rawa sai iko

Rubutawa: Zaharaddeen Ibrahim Katsina (Mayanan Safana)

 *AllahHu A'alam*