Jami’ar Al-Kalam Katsina Za Ta Gudanar Da Taron Yaye Dalibai Karo Na 16
- Katsina City News
- 02 Dec, 2024
- 224
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
Jami’ar Al-Kalam Katsina ta sanar da shirye-shiryen taron yaye dalibai karo na 16 wanda zai fara daga ranar Laraba, 4 ga Disamba, zuwa Asabar, 7 ga Disamba, 2024.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Nasiru Musa Yauri, ya bayyana cikakken bayani game da taron a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin sa dake jami'ar ranar Litinin biyu ga watan Disamba 2024
Farfesa Yauri ya jaddada jajircewar jami’ar wajen ci gaba da gudanar da taron yaye dalibai a duk shekara. A bana, za a yaye dalibai 1,433 daga karatun shekarar 2023–2024. Ga rabe-raben da aka yi:
- 22 sun samu digiri na farko da aka fi so (First Class Honours)
- 218 sun samu Second Class Upper
- 641 sun samu Second Class Lower
- 499 sun samu Third Class
- 53 sun kammala da Pass Degrees
Bugu da ƙari, za a ba da digirin digirgir (Ph.D) ga dalibai bakwai, biyu za su samu digirin MA/MSc, yayin da 12 za su samu digirin Professional Master’s.
Haka zalika Farfesa Yauri ya bayyana wasu muhimman Ayyuka kamar haka:
- Laraba, 4 ga Disamba: Bikin bude taron a filin kwallon jami’a da karfe 4:00 na yamma.
- Alhamis, 5 ga Disamba: Gasar karshe ta Musabaqar Karatun Al-Qur’ani da misalin karfe 10:00 na safe a zauren ICT.
- Jumma’a, 6 ga Disamba: Jawabin gabatarwa kafin taron yaye dalibai a dakin taro na Muhammad Lawal Kaita da misalin karfe 4:00 na yamma. Za a gabatar da jawabi daga bakin Farfesa Ahmad Bello Dogarawa kan maudu’in "‘Yancin Kasuwanci da Gyaran Haraji a Najeriya: Shin Yanayin Tattalin Arziki Ya Yi Daidai da Tsare-Tsaren Gwamnati?"
- Asabar, 7 ga Disamba: Babban taron yaye dalibai a harabar jami’a da misalin karfe 10:00 na safe, wanda zai hada da bayar da digirori da karramawa na musamman.
Daya daga cikin abubuwan jan hankali a bikin yaye daliban wannan shekarar shi ne gasar karatun Al-Qur’ani da aka shigar cikin al’adun jami’ar tun bara. Shugaban Jami’ar, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bada gudummawar naira miliyan 12 ga mahalarta gasar, inda zakarun maza da mata za su karɓi naira miliyan daya kowanne.
Digiri na Girmamawa
Jami’ar za ta ba da digirin girmamawa ga fitattun mutane hudu 'Yan Najeriya:
- Marigayi Umaru Musa Yar’adua: Tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma Shugaban Najeriya, wanda za a ba shi digirin Doctor of Letters.
- Marigayi Walin Daura Alhaji Sani Buhari Za a ba shi digirin Doctor of Business Administration.
- Alhaji Dahiru Barau Mangal: Za a ba shi digirin Doctor of Business Administration saboda gudunmawarsa ga kasuwanci da cigaban kasa.
- Alhaji Bilya Sanda (Khadimul Qur’an): Za a ba shi digirin Doctorate in Islamic Studies saboda jajircewarsa kan ilimin addini da hidimar al’umma.
Farfesa Yauri ya yi kira ga iyaye, tsoffin dalibai, da jama’ar gari su halarci wannan gagarumin biki. Ya ce, “Wannan wani babban lokaci ne na murna ga dalibanmu, iyayensu, da al’ummar jami’a. Muna fatan maraba da kowa don gudanar da wannan biki cikin farin ciki.”