Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bayyana Nasarori da Cigaban Da Ta Samu A Watannin Da Suka Shude Ga Manema Labarai
- Sulaiman Umar
- 29 Nov, 2024
- 175
Daga Sulaiman Ciroma
Gwamnatin jihar Katsina ta gabatar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da ta samu a watannin baya da suka shude.
Gwamnatin ta yi taron ne karkashin sabon tsarinta na bayyana nasarori da cigaban da ta samu a fannoni daban-daban a watannin baya kadan da suka shude ga jama'ar jihar Katsina.
Da yake jawabi, mataimakin gwamnan jihar Katsina Alhaji Faruk Lawal Jobe, ya bayyana inda gwamnatin jihar ta bada horo a fannin kwamfuta ga matasa 3,200 a kan Naira miliyan N333,811,788, sannan ta karrama wasu daga cikin gwarazan ma'aikata gwamnati masu aiki a karamar hukumar Katsina da sauran kananan hukumomin dake fadin jihar da lambar yabo da kuma kyaututtuka domin kara musu karfin gwiwa na irin kokarin da suke wajen aiwatar da ayyukansu.
Yayin cigaba da jawabin nasa, Alhaji Faruk Lawal Jobe ya sake bayyana inda gwamnatin jihar ta rabar da N957,345,000 wajen bayar da tallafin Ramadan ga kowane lungu da sako a fadin jihar tare da sallamar 'yan fansho.
Kazalika gwamnatin ta rattaba hannu tare da bada umurnin biyan bashin kudin giratuti na ma'aikatan da suka yi ritaya da ba a biya ba akan Naira N24,015, 785,518.6
Bugu da kari karkashin shirin KT-CARES gwamnatin ta kashe Naira N8,150,785,518.6 don bada gudunmawa ga mabukata masu karamin karfi.
Domin karin bayani game da wannan rahoto zaku iya bibiyar shafinmu na facebook mai suna 'KATSINA CITY NEWS'