Garin Kukar Babangida Na Neman Zama Kufai..
- Katsina City News
- 11 Sep, 2023
- 963
....Muna Neman a Kawo Mana Ɗauki ...Cewar Wani Mazaunin Garin.
Kukar Babangida babban gari ne da yake bisa kan hanyar zuwa ƙaramar hukumar Jibia dake jihar Katsina, kusan a iya cewa akan wannan hanyar Garin Magamar Jibia ne kaɗai zai iya kafada da kafada da Kukar Babangida wajen yawan Al'umma.
Kimanin mutane sama da Dubu Shidda ne suke rayuwa a wannan gari wanda yake da Mai Garin da ake kira Magaji Zaure ƙarƙashin hakimcin Sarkin Arewan Katsina hakimin Jibia, garin na Kuka yana ƙunshe da mutane sosai da suke noma da kiwo da sauran Sana'o'i na yau da kullum.
Kaɗan daga cikin ƙauyukan da suke zagaye da garin Kukar Babangida sun haɗa da; Takatsaba, Sanseri, Bihayyu, Jarkuka Babba Jarkuka ƙarama, Tantirai, Gangara hayi da Ƴargeza.
A halin yanzu anyi ittifaƙin cewa gaba ɗaya Mutanen dake zaune a ƙauyen ƴargeza ɓata gari ne masu satar Mutane da dabbobi duk Mutanen garin na kirki sun gudu sun bar garin domin tsira da rayuwar su da mutuncin su da na iyalan su.
Ƙauye na biyu da shima yake cikin tashin hankali shine Gangara hayi Mutane garin suna zama cikin fargaba ne a koda yaushe, da zarar sunga Baƙon mashin kowa zaiyi ta kanshi ne domin neman wurin ɓuya, Sati 2 daya wuce sun ɗauki mutum Ashirin 20 sun kashe Biyu 2 a ciki, Sauran Goma Sha Takwas 18 kuma sai da aka biya masu kuɗin fansa kowannen su Naira Dubu Arba'in 40 kafin a sake su.
Garin Kuka na daga cikin garuruwan da wannan Ibtila'in na rashin tsaro yake addaba Inda a halin yanzu ɓarayin suke cin karen su babu babbaka tare da yin yadda sukaga dama, dalilin da yasa da dama daga mutanen garin sukayi ƙaura zuwa wasu wuraren, wannan dalilin nema yasa muke roƙon gwamnati da jami'an tsaro suzo su kafa wani shingen Jami'an tsaro na bincike a garin hakan zai hana zuwan ɓarayin dajin kawo ma garin farmaki.
Ko a Ɗan tsakanin nan ɓarayin daji sun farmaki garin Inda suka kama wani yaron mai garin mai suna Jamilu bisa zargin yana baiwa ƴan Banga bayanai akan su, Inda suka yi mashi kisan wulakanci dalilin da yasa kowa yake taka tsantsan a garin, hatta mai garin wasu sun bashi Shawarar yin ƙaura yabar garin amma Al'umma suka Roƙi da kada ya tafi yabar su, madamar yabar garin toh lallai garin zai iya tarwatsewa, Inda yace Matuƙar dai jama'a na garin lallai babu inda zaya zasu ci gaba da addu'ar Allah ya kawo masu zaman Lafiya.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wani Matashi ne mai suna Sarki Wadanda shine yake Jagorantar ɓarayin dajin suke zuwa suna addabar garin na Kuka duk da yake shima Ɗan asalin garin ne tare da masu bashi bayanai wato Informers, dazarar sunga kana mu'amulla da ƴan Banga zasu zo har gida su tafi da kai, Yanzu haka akwai wani tsohon Ɗan banga dake garin shekaran jiya suka aiko mashi da sakon yana cikin wanda zasu kashe.
Yanzu haka dai Al'umma suna neman ɗauki na tsaro dama na buƙatun yau da kullum, Muna Adduar Allah ya kawo mana ƙarshen wannan Ibtila'in ya zaunar damu lafiya Amin.