Kungiyar PROWAN Arewa Maso Yamma Ta Rantsar da Sabbin Shugabanni Tare da Bayar da Kyaututtukan Girmamawa
- Katsina City News
- 09 Nov, 2024
- 154
A ranar Alhamis, 7 ga Nuwamba 2024, kungiyar Professional Women Accountants in Nigeria (PROWAN), reshen Arewa maso Yamma, ta gudanar da taron rantsar da sabbin shugabanninta a dakin taro na gidan gwamnatin jihar Katsina. Taron ya samu jagorancin Hajiya Fatima Muhammad Buhari, shugabar PROWAN ta jihar Katsina.
Taron ya samu halartar manyan baki, ciki har da shugaban kungiyar ANAN, Dr. James E. Neminebor; Hajiya Zuwaira Talatu Kishimi; Hon. Bashir Tanimu Gambo; da Alhaji Shu’aibu Aliyu. Jahohin da suke karkashin yankin Arewa maso Yamma, wato Katsina, Zamfara, da Kebbi, duk sun gabatar da sabbin shugabanninsu tare da yin rantsuwar kama aiki.
A jawabinta, Hajiya Fatima Muhammad Buhari ta mika godiya ga uwar kungiyar ta ƙasa bisa yadda aka gudanar da wannan muhimmin taro a Katsina. Ta kuma yi kira ga sabbin shugabanni su dukufa wajen gudanar da ayyukansu cikin jajircewa domin bunkasa kungiyar.
Shugaban ANAN na ƙasa, tare da mataimakiyarsa, da shugabar PROWAN na yankin Arewa maso Yamma, duk sun gabatar da muhimman jawabai, inda suka yi kira ga mambobin kungiyar su ci gaba da jajircewa wajen ciyar da kungiyar gaba.
A bangaren gwamnati, mataimakin gwamnan jihar Katsina, Alhaji Faruk Lawal Jobe, ya wakilci gwamna Malam Dikko Umar Radda a taron walimar cin abinci da aka shirya da daddare. A lokacin walimar, an bayar da kyaututtuka ga gwamnan jihar don girmamawa bisa gudummawar da yake bayarwa ga kungiyar.