Jadawalin Budgit Na 2024: Jihar Zamfara Ce Kan Gaba Wajen Tattara Kuɗaɗen Shiga Na Cikin Gida A Nijeriya
- Katsina City News
- 04 Nov, 2024
- 205
An sanya Jihar Zamfara a matsayin jihar da ke kan gaba a cikin Ayyukan Tattara Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida a Nijeriya (IGR) a kan rukunin A.
A wani rahoton wata ƙungiya mai bibiyar harkokin kasafin kuɗi da ake kira BudgIT na 2024, wanda aka ƙaddamar a makon da ya gabata a ranar Talata, bugu ne na shekara-shekara da ke kimanta ayyukan kasafin kuɗin kowace jiha na dogon lokaci da kuma ɗorewar kasafin kuɗin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa babban ci gaban da aka samu wajen bunƙasar kuɗaɗen shiga na jihar Zamfara da kashi 240.44% na da nasaba da matakin da jihar ta ɗauka na cewa ba wai kawai ta dogara ne kocokan kan kason kuɗin da take samu daga ga Gwamnatin Tarayya (FAAC) ba ne.
Sanarwar ta ƙara da cewa, rahoton na BudgIT ya samu ne ta hanyar nazari da tantancewa da kuma ƙididdigar ayyukan kasafin kuɗi na dukkan jihohi 36, daga mafi yawa zuwa mafi ƙaranci.
Rahoton na BudgIT ya bayyana gagarumin ci gaban da ake samu a jihar Zamfara ta hanyar tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), inda ya nuna cewa daga jiha ta 36 a shekarar 2023, Zamfara ta kai matsayi na 26 a shekarar 2024.
“Wannan gagarumin aikin za a iya danganta shi da yunƙurowar jihar bayan da ta samu koma baya na kashi 49.75 cikin 100 na IGR na shekarar 2022, inda ta ƙara da kashi 240.22% daga biliyan N6.51 a shekarar 2022 zuwa biliyan N22.16 a shekarar 2023.
“Ana samun ci gaban sosai a bangaren IGR na Zamfara duk shekara: Harajin ta na shiga ya ƙaru da kashi 142.26% daga biliyan N5.03 a 2022 zuwa biliyan N12.18, lasisi ya ƙaru da 5921.22% daga miliyan N22.78 a 2022 zuwa N1.37 Biliyan a 2023, Kuɗaɗen sun ƙaru da kashi 3610.38% daga miliyan N82.44 a 2022 zuwa biliyan N3.06 a 2023.
“Bugu da ƙari, tarar ta tashi da kashi 1924.52% daga miliyan N24.15 a 2022 zuwa miliyan N491.32 a 2023, ayyukan tallace-tallace ya ƙaru da kashi 32.49% daga miliyan N772.06 a 2022 zuwa biliyan N1.02 a 2023, abin da ake samu ya ƙaru da kashi 5.7% zuwa 582% a 2022 zuwa miliyan N562.48 a 2023, kuma abin da ake samu daga sauran haraji ya ƙaru da kashi 519.71% daga miliyan N412.03 a 2022 zuwa biliyan N2.55 a 2023.
“Bugu da ƙari kuma, jihar ta samu kuɗaɗen shiga daga hayar gine-ginen gwamnati, hayar filaye da sauran su da samun kaɗaɗe daga zuba hannun jari duk an shigar da su cikin kuɗaɗen shiga a shekarar da ta gabata. Zamfara za ta iya nuna aniyar inganta tattalin arzikinta ta hanyar binciko albarkatun ƙasa tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya don karkato da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
“Jimillar kuɗaɗen shigar jihar ya ƙaru da kashi 65.35% zuwa Naira Biliyan 144.95 a shekarar 2023 daga Naira Biliyan 87.68 da ta samu a shekarar da ta gabata. Dangane da tsarin kuɗaɗen shigar da ake samu akai-akai, alamun masu ƙarfi sun nuna cewa jihar na fuskantar raguwar samun kuɗaɗen shiga daga shekarar da ta gabata yayin da dogaro kacokan kan kason kuɗin da take samu daga Gwamnatin Tarayya daga kashi 90.52% a shekarar 2022 zuwa kashi 74.66% a shekarar 2023, duk da rabon kuɗin da kashi 4.93% daga biliyan N62.21 zuwa biliyan N65.28. A ƙarshe, Ayyukan Tattara Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida a Nijeriya (IGR) zuwa rabon kuɗaɗen shiga na yau da kullum na 2023 ya kasance kashi 22.16% sama da kashi 9.48% a cikin 2022.