Kungiyar Masu Sana'ar Kayan Gwangwani A Katsina Ta Rantsar Da Shugabanninta Na Jihar.
- Katsina City News
- 02 Nov, 2024
- 387
Auwal Isah (Katsina Times)
Kungiyar nan ta Masu Sana'ar Kayan Nauyi a jihar Katsina, NASWED, ta yi bikin kaddamarwa tare da rantsar da shugabanninta da masu Sa-ido na jihar.
Bikin rantsarwar wanda aka yi a dakin taro na hukumar Ma'aikatan karamar hukumar Katsina a ranar Asabar din nan, ya samu halartar Membobin kungiyar a daukacin jihohin Arewa da matakin Kasa baki daya.
Tun farko kafin kaddamar da Membobi, masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro, Shuganni da hukumomin gwamnati sun fara gabatar da Lakcoci a taron, inda suka bayyana jin dadinsu da kafa wannan kungiya da masu Sa'idonta don tsaftace ta, duba da yadda ake yawan samun korafe-korafe kan irin ta'annatin da ake zargin wasu bara-gurbin masu sana'ar na yi wa kayan al'umma da Kadarorin gwamnati, wanda hakan ya sa har ma wasu bata gari da suka shigo cikinsu suna yin sace-sace da sunan sana'ar.
Kungiyar wadda ta samu halartar shugabanta na yankin Arewa, Honorabul Alhaji Aminu Soja, ya yi jawabin tare da bayyana matakan da suka dauka na tsaftace sanar'ar, inda ya bayyana cewad duk dan kayan nauyin da aka kama da sayen kayan Sata ko kadarar gwamnati, to za su hannata shi ga hukuma ba sani ba sabo.
Sannan ya bayyana yadda suka dauki masu aikin Sa-ido a boye a cikin kungiyar, wadanda za su taya jami'an tsaro zakulo masu wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban Kuliya.
Kungiyar har wayau, ta kuma bukaci dukkan wani Sana'ar Kayan nauyi, Gwangwani, Jari-bola duk inda yake a cikin jihar, ya tabbatar ya yi rajista da kungiyar don a tabbatar da ko shi waye, kafin su fara daukar matakin wadanda ba su da rajistar a nan kusa.
Kungiyar ta NSWEN, ta rantsar da Alhaji Mustapha Sulaiman a matsayin shugaban 'yan gwamgwanin jihar Katsina, yayin da Kabir Bala Mashi ya zama mataimakinsa da sauran mukamai.
Sauran wadanda za su dafawa shugaban wajen gudanar da kungiyar a matakin kananan hukumomin jihar 34 sun hada da: Hasan Isah Daura a matsayin shugaban kungiyar na karamar hukumar Daura, Abdullahi Bala a matsayin shugaban kungiyar na karamar hukumar Funtua, Muhammad Aminu a matsayin shugaban 'yan Sintiri da Sa-ido a hukumar, da sauransu.
Hakazalika, taron rantsarwar ya samun halartar Alhaji Surajo Lawal kwaskwaro Danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Kaita, Dr. Lawal Habibu babban Darakta mai kula da hukumar kadarorin gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Shehu SPC Kaduna da sauran muhimman mutane.
Sauran mahalartartan sun hada Jami'an tsaro, 'yan jarida, 'yan wasan kwaikayo Makada da Mawaka da sauransu.
Haka nan kuma, duk a wajen bikin rantsarwar an karrama tare da ba da kyauta ga wasu zakakuran Membobin kungiyar don sauran membobi su yi koyi da su halayensu.