GWAMNA DIKKO RADDA NA JIHAR KATSINA YA UMURCI A SAKE SHATA BURTALI DA FITAR DA MUTANEN DA SUKA YI NOMA A KAN LABI DA DAZUZZUKAN GWAMNA BA BISA KA'IDA BA.
- Katsina City News
- 29 Sep, 2024
- 231
28/9/2024
Gwamnan Jihar Kastsina, Malam Dikko Umaru Radda ya umurci shugabannin Kanan Hukumomin Zango da Mashi da su fitar da Manoman da suka ci gandun daji da burtali dake yankunansu ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnan ya bada umurnin ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari wanda ya ziyarci kananan hukumomin don tantance koken da wasu makiyaya su ka yi cewa wasu mutane sun nome wuraren da suke bi da kuma kiwon dabbobinsu.
Sakataren Gwamnatin ya yi bayanin cewa a sakamkon korarafe - korafen da Fulani makiyaya 'yansalin yankin suka rubuto, ya yi zama da dukkan bangarorin biyu tare da shugabannin kananan hukumomin a ofishinsa.
Alhaji Abdullahi Faskari ya ce ya zo ne da kan shi domin gane ma idonsa gaskiyar abinda ke faruwa.
A karamar hukumar Zango an zagaya inda wani rahoto ya nuna an ci labi to amma ba a ga shedar yin hakan ba.
Sai dai kuma wakilin shugaban Kungiyar Miyyeti Allah na kamar hukumar ya kai tawagar Sakataren Gwamnatin wani daji dake bakin gari inda aka samu cewa wani manomi ya fadada gonarsa har cikin dajin Gwamna.
Saboda haka Alhaji Abdullahi Faskari ya ba shugaban karamar hukumar Alhaji Babangida Aliyu Yardaje umurnin a gano mai gonar a ji a ina ya samu izinin noma dajin, kana ya bada umurnin a gaggauta share duk inda ya noma ba bisa kaida ba.
A dajin Atakar dake Mazabar Tamilo a karamar hukumar Mashi ma, Fulani mazauna yankin sun kai tawagar Sakataren Gwamnatin a cikin dajin yankin inda suka nuna masa yadda wasu mutane ke ta sassabe dajin baji - ba - gani.
Sai dai kuma tawagar ta yi kicibis da wani da ake margin ya falli dajin mai suna Alhaji Bello wanda ya ce shi mutumen Safana ne amma wai yana da takardar sheda da wani Maigari ya ba shi.
Jin hakan ya sanya Sakataren Gwamnatin ya umurce shi da ya kawo kwafen takardar a ofishinsa domin a gudanar da bincike.
Bugu da kari kuma an samu wani labi da wani manomi ya datsa, ya hada da gandun dajin ya nome.
Da aka waiwaiyi shugaban karamar Mashi Alhaji Salisu Kalla Dankada ya ce duk baya da masaniya akai.
Don haka a nan take Sakataren Gwamnatin ya ba shi kwanaki uku da ya tabbatar sashen aikin gona na karamar hukumar ya je fidda labin kamar yadda ya ke a da.
Alhaji Abdullahi Faskari ya sauran sassan dajin da mutumen ya diba kuma za a neme shi ya yi bayani.
Daga nan ya gargadi jama'a musamman masu sha'awar yin noma da su sani cewa Gwamnan Jiha ne kadai ke da ikon bada bada kasa ko daji don yin wani abu a duk fadin jihar nan.
Ya ce gwamnati na daukar wadan nan matakai ne don kauce ma irin abubuwan da suka haddassa matsalar rashin tsaro a wasu sassan Jihar nan.
A Maiaduwa kuwa, Sakataren Gwamnatin ya amince da yarjejeniyar da ya tarar an kulla tsakanin Fulanin da suka kawo koken da kuma Manoman da suka cinye dajin kiwo na Mululu da Jirdede da Bakin boda cewa sun yi masu rangwame su girbe amfanin da suka riga suka shuka a yayin da su kuma Manoman suka yi alkawarin za su bar masu karan da harawar su ciyar da dabbobinsu tun dama dajin an tanade shi ne don makiyaya. Amma daga bana ba wanda zai kara noma shi.
A nan din ma ya bada umurnin a kaddamar da bincike akan wani mutum da aka ce ya zo daga wata makwafciyar jiha, ya kafci hekta 70 a cikin wata makiyaya da sunan wai an ba shi ne, zai yi kamfani.
A can Kaita kuma, manoma sun mamaye dajin 'Yanhoho da labin da makiyaya ke bi zuwa mashayar dabbobi.
Sai dai Manoman sun yi ikirarin cewa Sashen kula da gandun daji na Jiha ya ba su haya, abinda Sakataren Gwamnatin ya ce wannan tsari haramtacce ne, don haka umurnin Gwamna ya soke shi.
Anan ma Makiyayan sun hakura cewa a kyale wadanda suka yi shukar su girbe amfanin su.
A can dajin Judi dake Karofi kuma a karamar hukumar Dutsinma, Sakataren Gwamnatin ya shiga tsakanin mujadalar da ta sarke tsakanin Fulanin yankin da wani mai suna Onarabul Aminu wanda suke zargi da mamaye mashaya da burtali da gandun dajin dake yankin.
Tun farko Ardon Fulani, Muhammadu Bello Fulani wanda ya jagoranci rubuta takardar koken ga Ofishin Sakataren Gwamnatin ya nuna masa yawan barnar da suke zargin an yi masu.
Sun sheda cewa shekara aru -aru duk Makiyayan yankin da baki masu wucewa ta nan su ke bi, su ciyar su kuma shayar da dabbobinsu, amma bana sun rasa yadda za su yi.
Da Ardon da Maigarin da kuma Shugaban rikon karamar hukumar ta Dutsinma, Alhaji Sada Ibrahim Sada duk sun tabbatar da cewa 'Yandakan Katsina, Hakimin Dutsinma ya rubuto ma Aminu da sauran Manoman da su tashi daga wurin amma suka ki.
Shi Aminun ya kafe akan cewa wai wani tsohon shugaban karamar hukumar ne ya ba shi wurin.
Daga karshe dai Sakataren Gwamnati Abdullahi Garba Faskari ya umurci Shugaban rikon karamar hukumar da gaggauta sake shata burtalin, ya kuma kakkafa turakun kan iyaka masu karfi.
Na biyu kuma su zauna da bangarorin biyu a samu masalaha don barna biyu ba ta yin daidai guda daya.
Amma ya ja kunnen su cewa badi duk wanda ya kuskura ya shiga wuraren da sunan shuka to, ya kuka da kansa.
Ya kuma yi bayanin cewa ofishinsa zai ci gaba da zagayawa domin warware irin wadan nan matsaloli a duk inda aka samu rahoton cewa akwai su a duk fadin jihar nan.
A dukkan yankunan da aka ziyarta Fulani Makiyayan sun yi godiya ga Gwamna Dikko Umaru Radda akan wannan mataki da ya dauka don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su da 'yanuwansu Manoma.
Sun yi alkawarin ci gaba da bada goyon baya da hadin ka ga tsare tsare da manufofin Gwamnatin Jihar Kastsina.
A cikin tawagar Sakataren Gwamnatin akwai Babban Sakatare a Sashen Tsaro da Sha'anin Mulki, Alhaji Salisu Abdu da Daraktan Watsa Labarai, Abdullahi Aliyu Yar'adua da Mukaddashin Daraktan Tsaro Alhaji Hamza Audi Kofarbai da dai sauransu.
Abdullahi Aliyu Yar'adua,
Director of Press,
SGS Office.