Kwamitin Bincike ya Miƙa Rahoton Gobarar Fadar Gwamnatin Jihar Katsina
- Katsina City News
- 10 Sep, 2024
- 363
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times Satumba 10, 2024
Kwamitin bincike da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya kafa don binciken gobarar da ta auku a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, ya miƙa rahoton bincikensa ga Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari.
Kwamitin da shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ke jagoranta, an ɗora masa alhakin gano musabbabin gobarar da kuma samar da shawarwari domin hana aukuwar irin haka nan gaba. Gobarar, wadda ta faru a dakin taro na saman bene da ke kusa da ofishin mai girma gwamna, ta faru ne a ranar 3 ga Satumba.
Yayin miƙa rahoton, Alhaji Bawale ya bayyana yadda kwamitin ya fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba, inda suka duba wurin da gobarar ta auku tare da gudanar da muhimman tambayoyi ga ma’aikatan da abin ya shafa. “Mun gayyaci mai taimaka ma mai girma gwamna, (ADC) jami’an tsaro da ke aiki a lokacin da gobarar ta faru, da kuma injiniyan da ke kula da CCTV na fadar gwamnati, da sauransu. Shigar tasu ya taimaka ƙwarai wajen haɗa cikakken rahoton,” in ji shi. Bawale ya ƙara da cewa, kwamitin ya sami sa’a kasancewar wasu mambobi sun kasance a wurin da gobarar ta faru, wanda hakan ya taimaka sosai wajen binciken.
Rahoton kwamitin ya haɗa da cikakken jerin kayan da gobarar ta lalata, da kuma muhimman shawarwari don inganta matakan kariya daga gobara a Fadar Gwamnati da wasu wurare masu muhimmanci na gwamnati. “Rahotonmu ya cika kuma ya taɓo dukkan batutuwan da suka dace. Muna fatan shawarwarinmu za su taimaka wajen hana faruwar hakan nan gaba,” in ji Bawale.
A jawabin sa, Barista Abdullahi Garba Faskari, a madadin Gwamna Radda, ya nuna godiya ga ƙoƙarin kwamitin da saurin miƙa rahoton cikin lokaci. “Gwamnati na shirye ta duba kuma ta aiwatar da shawarwarin da aka bayar domin kare kadarorinmu,” in ji Faskari. Ya yaba wa kwamitin bisa jajircewarsu, tare da tabbatar musu cewa aikin da suka yi ba zai tafi a banza ba.
“Na aminta da kwamitin tun farko,” Faskari ya ci gaba da cewa, “kuma na yi farin ciki da samun rahoto mai tsari da cikakken bayani. Gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa ba.”
Sakataren Gwamnatin Jihar ya rufe taron da godiya ga kwamitin bisa sadaukarwarsu, yana mai cewa aikinsu zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsare-tsaren kare lafiyar kadarorin gwamnati a fadin jihar Katsina.