Rundunar 'Yansanda Ta Kama Masu Laifuka Daban-daban Har 22 A Katsina
- Katsina City News
- 05 Sep, 2024
- 354
Katsina Times, 5 ga Satumba, 2024
Rundunar ’yan sanda ta jihar Katsina ta sanar da kama mutane 22 da ake zargi da aikata laifukan sata da lalata kayayyaki a jihar.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa an kama waɗannan mutanen ne a cikin wasu Samame guda uku daban-daban da aka gudanar tsakanin 24 ga Agusta zuwa 5 ga Satumba, 2024.
A farkon samamen, an kama mutane uku - Hamza Lawal, Safiyanu Usman, da Mariya Adamu - waɗanda ake zargi da satar kayayyaki masu darajar Naira miliyan 10 daga wani gida a unguwar Modoji, Katsina.
A Samame na biyu, an kama mutane 12 waɗanda ake zargi da lalata manyan wayoyin wutar lantarki a cikin birnin Katsina.
A Samame na uku, an kama mutane shida waɗanda ake zargi da lalata magudanar Ruwa ta Kofar Marusa tare da satar Rodin dake cikin ginin
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa ta kwato wasu kayayyaki, ciki har da waɗanda aka sace, wayoyin lantarki, Rodiddika, da kuma kayan aikin da aka yi amfani da su wajen lalata kayayyakin.
A halin yanzu, ana ci gaba da bincike kan mutanen da aka kama, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran abokan aikinsu da suka gudu.
Rundunar ’yan sanda ta jinjina wa al’umma bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da laifuka a jihar.