DAGA RANAR 15 GA WATAN SATUMBA,BABU LAYIN DA ZAI KARA AIKI IN BAIDA CIKAKKIYAR RIJISTA.
- Katsina City News
- 29 Aug, 2024
- 222
sanarwar manema labarai
.....INJI HUKUMAR NCC
.....Anyi ma sama da layu milyan 153 rijista
Fassarar Hassan M Tukur
@Katsina Times
Hukumar Bin diddigin Ayyukan Kamfanonin Sadarwa tana farin cikin shaida ma al'umma cewa an samu cigaba Mai Ma'ana na aiwatar da tsarin da Gwamnatin Tarayya ta bullo da Shi na hada lambar katin dan kasa da lambar layuyyukan masu buga waya.
Ya zuwa yanzun Sama da layuyyukan milyan 153 ne na wayoyi aka hada da katin Dan kasa , Wanda ya nuna samun biyayya ga wannan Shirin na Kashi 96 bisa dari, Wanda ya zarce na Kashi 69.7 bisa dari da aka samu a Watan Janairu na shekarar 2024.
Yayin da akazo Kan gabar kammala wannan tsari, Hukimar bin diddigi na ayyukan kamfanonin sadarwa na sake neman hadin Kan 'Yan Najeriya domin a cinma nasarar Kashi dari bisa dari na kammala wannan tsari na hada layuyyukan 'Yan kasa da lambar katinsu Na Dan kasa.
Hada katin Dan kasa da lambar layuyyukan wayiyinsu zai inganta tsaro da inganta hanya sabuwa ta bunkasa tattalin arziki.
Ta hanyar gane layuyyukan wayoyin _Yan kasa Zai inganta cinikayya ta hanyar yanar gizo -gizo ta Zamani da rage kafafen cutar Al' umma da aikata laifuffukan zamba , da inganta cinikayya ta Zamani da hanyar gudanar da bankuna da tafiyar da kudade ta salula. Wannan Zai kawo tafiyar da tattalin arziki na bai daya a kasa
Ta hanyar hadin gwiwa da ofishin Mai ba Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro da Hukumar Rijistar katin Dan kasa da Hukumar bin diddigi na ayyukan kamfanonin sadarwa an gano abun damuwa yadda wadansu 'Yan Najeriya suka mallaki layuyyukan wayoyi masu tarin yawa da zimmar aikata laifuffukan zamba da suka layuyyuka dubu dari.
Hukumar bin diddigi na ayyukan kamfanonin sadarwa ta sha alwashin yin aiki kafada da kafada da jami'an tsaro da Sauran masu ruwa da tsaki domin danko masu sayarda layuyyukan wayoyi da basu da Rijista domin inganta tsaro da maido martabar layuyyukan wayoyi a idon duniya.
Domin kammala wannan tsari na hada layuyyukan wayoyi da katin Dan kasa, Hukumar bin diddigi na ayyukan kamfanonin sadarwa ta ummarci dukkan kamfanonin sadarwa da su tabbatar an kammala wannan tsari nan da zuwa sha hudu ga Watan satumba na shekarar 2024.
Daga satumba sha biyar ga wata, Hukumar zata tabbatar da babu Wani layin waya marar rejista da zai yi aiki a Najeriya.
Hukumar na kira ga daukacin al'umma wadanda basu da Rijista da su ziyarci ofishin kamfanin su na sadarwa domin danganta kowane layi da katin Dan kasa kafin waccan rana ta sha biyar da aka Kebe don kammala Rijista.
Bugu da Kari akwai layukan da aka bude na yanar gizo -gizo don dangata layuyyukan wayoyi da katin Dan kasa da kanku.
Hukumar bin diddigi na ayyukan kamfanonin sadarwa ta na tunatar da 'Yan kasa cewa sayen Kati maras Rijista laifine da Zai ja a daure Ko Cin tarar Mai aikata laifin.
Ana shawartar 'Yan Najeriya da su bada rahoton masu saye da sayar da layuyyukan wayoyi maras Rijista ga jami'an Hukumar ta layin waya Mai lamba 622 Ko kafofinta na sabuwar hanyar sadarwa na Zamani.
Hukumar na godiya da cigaba da samun goyon baya ga ayyukan ta na inganta yanayin buga waya ba tare da matsaloli ba.
Reuben Muoka
Daraktan kula da sadarwa
29/08/2024