Yan sanda sun gayyaci shugaban NLC Joe Ajaero kan zargin aikata laifukan Cin Amanar Ƙasa
- Katsina City News
- 19 Aug, 2024
- 329
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta bakin ofishin Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda, reshen Hukumar Binciken Sirri (IRT), ta gayyaci shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi hada baki don aikata laifi, tallafawa ayyukan ta'addanci, cin amanar kasa, da kuma aikata laifuka ta hanyar yanar gizo.
A cikin wasikar gayyatar da aka aikawa Ajaero, an bukaci ya bayyana a gaban ofishin IRT da ke unguwar Gwari Gwaɓi, Abuja, a ranar Talata, 20 ga watan Agusta, 2024, da misalin karfe 10:00 na safe, domin amsa tambayoyi game da binciken da ake yi. An kuma sanar da shi cewa idan har ya kasa amsa wannan gayyata, rundunar za ta dauki matakin fitar da sammacin kama shi.
Kwamandan IRT ya kuma bukaci Ajaero ya tuntubi jagoran tawagar binciken a lambar wayar da hukumar ta bayyana domin karin bayani game da wannan bincike.
Wannan matakin na zuwa ne bayan an ambaci sunan Ajaero a cikin wani bincike mai tsanani da ke gudana wanda ke da alaka da ayyukan ta'addanci da cin amanar kasa. An gargadi shugaban NLC kan cewa rashin halartar wannan gayyata zai iya haifar da fitar da takardar kama shi.