YANBINDIGA SUN HALLAKA HADIMIN GWAMNA DA MATARSA
- Katsina City News
- 17 Aug, 2024
- 495
Alhaji Sanusi Ango Gyaza shi ne wakilin Gwamnan jihar Katsina Mal. Dikko Umar Radda ( liaison officer) a karamar hukumar Kankia, kuma ya taba zama shugaban kungiyar Malaman makaranta (NUT) ta karamar hukumar Kankia.
Jiya Juma'a da misalin karfe 10 na dare barayin daji masu garkiwa da mutane suka afka masa har cikin gidansa da ke garin Gyaza ta karamar hukumar Kankia inda suka hallakasu shi da matarsa, kuma suka yi awon gaba da dayar matarsa da niyyar yin garkuwa da ita domin neman kudin fansa.
Kamar yanda kangiwa 360 ta samu labari zaa yi masu Sutura yau asabar da karfe 9 na safiyar nan.
Allah ya jikansu ya toni asirin duk wanda ke da hannu a cikin wannan aika aika.
Munciro daga shafin kangiwa 360