Ziyarar Mataimakiyar shugaban Ƙasa: An buƙaci Kara Karfafa Tsaro da Gyara Hanyoyi a Jihar Katsina

top-news

Katsina Times

Gwamnatin Tarayya ta samu kiran kara karfafa tsaro a jihar Katsina tare da gyara hanyar daga Funtua, Dandume zuwa Birnin Gwari. Wannan kira ya fito ne a wani taro na jin ra'ayoyin jama'a game da aiyukan raya mazabu da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa a jihar Katsina, musamman aiyukan da basu kammalu ba.

A taron da aka yi karkashin jagorancin Ofishin Mai Taimakama Shugaban Ƙasa akan Aiyukan Raya Mazabu, Hajiya Khadijat Omotoyo Kareem, ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Ahmed Tinubu na da ƙudirin kawo ci gaba ga ƙasar nan. Ta yi kira ga 'yan Najeriya su kara baiwa Shugaba Tinubu lokaci domin aiwatar da kudurorin cigaba da yake da su.

Hajiya Khadijat ta godewa Gwamnatin Jihar Katsina akan tarbar da suka yi mata tare da nuna godiyarta ga Shugaban Ƙasa akan damar da ya bata domin gudanar da aiyyukanta.

A jawabin shi, Mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Hon Faruk Lawal Jobe, ya jinjina wa mutanen jihar Katsina bisa dattaku da sanin ya kamata, wanda ya hana su shiga zanga-zanga. Ya bukaci Mai Taimakama Shugaban Ƙasa da ta kai dukkanin abubuwan da al'umma suka gabatar domin daukar matakin gaggawa daga Gwamnatin Tarayya.

Daga cikin mahalarta taron akwai Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare na Jihar Katsina, Dakta Faisal Kaita, wanda ya yi tsokaci akan aiyukan da suke bukatar a kammala, ciki har da gina hanyar mota mai hannu biyu daga Kano zuwa Katsina, da hanyar jirgin kasa daga Najeriya zuwa Nijer.

An kuma tattauna batutuwan da suka shafi gina madatsun ruwa, hanyoyin karkara, tsaro, noma da kiwo, cigaban mata da matasa, da kuma maido da shirin ciyar da dalibai da N-Power da shirye-shiryen tallafi. 

Taron ya samu halartar 'yan majalisar zartarwa na jihar Katsina, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin kungiyoyin fararen hula, uwayen kasa, sarakuna da sauran al'umma.

NNPC Advert