Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Katsina shugaban hukumar gudanarwa Ta TETFund
- Katsina City News
- 06 Aug, 2024
- 549
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin tsohon gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari da wasu shahararrun 'yan Najeriya shida domin su yi aiki a kwamitin gudanarwa na Tertiary Education Trust Fund (TETFund).
Cikin wata sanarwa da babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Chief Ajuri Ngelale ya sanya hannu kuma ya miƙa wa manema labarai, ya bayyana cewa: Aminu Bello Masari zai zama shugaban kwamitin, Sanata Sani Danladi mamba, Mr. Sunday Adepoju mamba, Mr. Nurudeen Adeyemi mamba, Mrs. Esther Onyinyechukwu Ukachukwu mamba, Mr. Turaki Ibrahim mamba da Mr. Aboh Eduyok mamba.
Shugaban ƙasa na sa ran sabbin 'yan kwamitin za su ba da himma da ƙwazo wajen cimma burin TETFund na samar da tallafi ga manyan makarantu domin inganta ƙwarewa da ingancin ilimi a matakin gaba da sakandare.