Tatsuniya Ta 41: Labarin Musare Da Hodanego
- Katsina City News
- 05 Aug, 2024
- 314
Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani mutum mai mata biyu, da 'ya'ya biyu. Uwar gidan tana da danta mai suna Musare; amaryar kuma tana da 'ya mai suna Hodanego. Ana nan har yara suka girma. Shi mahaifinsu yana da dabbobi masu yawa, sai ya ba Musare akuya guda, ita kuma Hodanego da take yarinya, ya ba ta kaza.
Suna nan, duk sanda Musare ya nemo wa akuyarsa abinci ya zuba mata, sai Hodanego ta saki kazarta ta je ta watsar da abincin. Kullum haka, har rannan yunwa ta kashe akuyar Musare. Ya yi hakuri bai ce komai ba, amma kuma kullum kanwarsa ta rika yi masa dariya, tana tsokanar sa. Daga karshe dai sai ya dan yi magana, sai uwar Hodanego ta kama shi da duka. Amma saboda kara irin ta matan kirki, mahaifiyarsa ba ta ce komai ba.
Wata rana sai uwar Musare ta kwanta ba lafiya, har jikinta ya fara rubewa ta fara wari, sai kishiyarta ta fara yi mata tsiya da 'yan maganganu, har da zagi tana cewa ita fa wari ya fara damun ta a gidan. Haka dai, kullum sai Musare da mahaifiyarsa su shiga daki su yi ta kukan bakin ciki. Da ciwo ya tsananta, sai ta ce da shi: "Ka tashi ka shiga dajin nan ka nemo mini magani."
Sai ya ce da uwarsa: "To." Washe-gari da sanyin safiya ya fita, ya kama hanyar dajin don nemo magani. Yana cikin dokar daji sai ya hadu da wata tsohuwa ita kadai tana dogara 'yar sanda. Da ta ji motsinsa sai ta ce: "Don Allah dan nan ka taimake ni ka dora ni kan hanya wadda zan bi in shiga gari."
Sai ya dube ta cikin murya lallausa ya ce: "Ayya, ai kin baro hanyar da nisa, amma bari in kai ki." Tsohuwa ta ce: "Yawwa, na gode." Ya shiga gaba, tana biye da shi har suka isa hanya. Sai tsohuwa ta ce da shi: "Dana da ma ina so in gwada kirkinka ne, kuma zan taimake ka a kan abin da ka fito nema."
Mamaki ya kama Musare, sai ya ce: "To." Sai tsohuwa ta ci gaba da yi masa bayani ta ce: "Ka bi wannan hanyar, kada ka tsaya har sai ka tarar da wata babbar tsamiya, sai ka tsuguna a gindinta ka roki duk abin da kake so."
Musare ya yi mata godiya, ya bi inda ta nuna masa har ya isa gindin tsamiyar da ta kwatanta masa. Musare na isa ya tsuguna, ya roki maganin ciwon da ke damun mahaifiyarsa. Sai kawai ya ga kullin magani ya fado daga wata sheka da ke kan tsamiyar. Ya dauka ya yi kamar zai mike tsaye, sai ya ji an ce: "Idan kana da wani abu da kake bukata, ka tambaya a ba ka."
Ya waiga bai ga kowa ba, amma sai ya ce: "Ciwon da ke damun uwata ne kan gaba da komai; maganin nan ma ya isa. Na gode." Kafin ya gama rufe baki sai ya ga an fito masa da wani doki ya sha ado da gwalagwalai da kayan sawa iri-iri da dukiya mai yawa, sai ya ji an ce: "Dokin da kayan nan duka naka ne."
Ya sake dubawa bai ga kowa ba, sai ya sake yin godiya. Da ya lura dai an sallame shi, sai ya dare kan doki, ya kama hanya bai zame ba sai gida, ya shiga ya daure doki, ya doshi dakin mahaifiyarsa. Da ya shiga dakin sai ya tarar saboda karfin maganin da aka ba shi, har mahaifiyarsa ta warke. Sai ya ba ta labarin yadda suka yi da tsohuwa. Ita kuma ta gaya masa cewa kishiyarta ma bayan tafiyarsa ta kamu da irin ciwon. Mahaifiyarsa ta yi masa godiya, kuma ta umarce shi da ya kai wa kishiyarta maganin ita la sha. Nan take ya dauki maganin ya fita tsakar gida, ya kira Hodanego ya ba ta maganin ta kai wa mahaifiyarta. Da kishiyar uwar ta karbi maganin ta sha, kuma nan take ta warke. Wannan lamari ya sa ta shiga cikin wani hali na jin kunya, sai kawai ta fashe da kuka, ta tashi ta shiga dakin uwar Musare tana ba ta hakuri. Ita kuma ta ce da ita ta yafe mata. Da haka suka ci gaba da zama gidan mijinsu, kamar 'yan uwa, ba sauran kishi. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kyakkyawar tarbiya jari ce ga mai ita; sai mai tarbiyar kwarai ne yake yin afuwa.
- Idan ka ga mutum mugu kuma maketaci to da ma ba shi da tarbiya.