'Yan Sanda a Katsina Sun Karyata Bidiyon da ke Yawo na Ikirarin Harbin Jami'in yayin Zanga-Zanga
- Katsina City News
- 03 Aug, 2024
- 343
Maryam Jamilu Gambo, Katsina Times
Katsina, 3 ga Agusta, 2024 — Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Katsina ta musanta wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta, musamman a X (wanda aka fi sani da Twitter), da ke ikirarin cewa wani dan sanda ya harbi abokin aikinsa har lahira yayin kokarin tarwatsa masu zanga-zanga a Katsina.
Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Katsina AA Musa, ya jaddada, "Babu asarar rai da aka samu a Katsina yayin zanga-zanga; "mu mai da hankali ga sahihancin labarai." Inji shi.
"Rundunar ta bayyana cewa bidiyon da ake magana akai na nuna wani jami'in tsaro kwance baya motsi, an sauya shi kuma an fitar da shi daga mahallinsa. Akasin ikirarin bidiyon, babu wani harbin da ya faru a yayin zanga-zangar. Jami'in tsaro da aka nuna a bidiyon jami'in NSCDC ne wanda ya fadi daga motar sintiri saboda hatsari da ya faru a wajen zanga-zangar. An garzaya da shi zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya a Katsina, inda aka kula da shi kuma aka sallame shi." Inji sanarwar
ASP Abubakar Sadiq Aliyu, Jami'in Hulda da Jama'a na 'Yan Sanda (PPRO), ya yi kira ga jama'a su yi watsi da wannan bayanin da aka karkatar kuma su tabbatar da sahihancin bayanai ta hanyar kafofin hukuma. Suna kuma tabbatar da karfi da hadin gwiwar da suke da shi da sauran hukumomin tsaro a jihar wajen kula da tsaro da zaman lafiya tare da aiwatar da ayyukansu cikin kwarewa. Rundunar na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Katsina.