Tatsuniya ta (21) Labarin Kurege, Maciji kura da Alade
- Katsina City News
- 30 May, 2024
- 429
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani lokaci da aka yi yunwa, ba abinci. Wuya ta sa Kura da Maciji da Alade da Kurege suka hada kai, suka hadu domin su hada gwiwea su yì noma tare. Sai suka zabi wani fili a dajin da suke, suka gyara. va o
gonarsu.
Ana nan, jim kadan kafin damina ta fadi, sai Maciji ya ce shi ne zai sassabe, watau zai gyara gona, ya sare lallagowa ya kawar da yayi.
Alade ya ce: "Ni zan yi mana huda.
Kura ta ce: Ni zan nome mana gonar.
Kurege kuwa sai ya ce: Ni kuma zan nemo mana irin shukawa."
A daidai lokacin da ya dace, sai Maciji ya tuge bishiyoyin gonar ya kone.
Alade ya yi musu huda. Kura ta nome.
Kurege ya tafi neman irin shuka a kasuwa, sai ya ga wata mata ta tara dawa da masara da gyada da wake. A daidai lokacin da ta tashi tafiya gida sai Kurege ya ruga, ya je gabanta ya kwanta kamar ya mutu.
Da matar ta gan shi sai ta ce: "Kai ga nama ya samu. To amma fa idan na dauka zai cinye mini dawa ta kare da wuri." Sai ta tafi ta bar Kurege, ba ta dauka ba.
Da Kurege ya ga haka sai ya tashi ya kama gudu, ya sha gaban matar nan ya kwanta.,
Da ta ga wannan Kuregen ba ta san na baya ba ne sai ta ce: "Allah ne ya ba ni"
Sai ta dauki Kurege ta sa a bakin kwaryarta, ta shiga gefen daji domin ta samo bawon kargo ta daure Kuregen ko ta ji dadin tafiya da shi gida.
A lokacin da ta ajiye kwarya ta je dayo bawon kargo sai Kurege ya dauki kwaryar nan cike da irin dawa ya gudu.
Da matar nan ta dawo, sai ta ga ba kwarya, ba Kurege. Hankalinta ya tashi, kuma ranta ya baci.
Haka dai matar nan ta kama hanyar gida da dan abin da ba a rasa ba, tana kuka.
Shi kuwa Kurege ya kai iri suka shuka tare da abokan nomansa.
Kurunkus.
Munciro wannan labarin daga Littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman