Ƴan ta'addar daji sun halaka Mutane a ƙananan hukumomin Malumfashi da Bakori Jihar Katsina
- Katsina City News
- 27 May, 2024
- 484
Kimanin sama da Mutane Talatin ne suka rasa rayukan su a ƙananan hukumomin Malumfashi da Bakori a jihar Katsina sanadiyyar harin ta'addanci na ƴan ta'addar daji.
A satin da yake fita ɓarayin dajin suka kai farmaki a ƙauyen ƴarteba dake cikin ƙaramar hukumar Malumfashi Inda suka halaka kimanin Mutane Goma Sha Bakwai basu ji ba basu gani ba.
Kazalika a ƙaramar hukumar Bakori da safiyar ranar Lahadi 26-05-2024 acikin garin lamido dake gundumar Guga ƙaramar hukumar Bakori an yi jana'izar Mutane Goma Sha Ukku da harin ta'addanci ya rutsa dasu.
Kimanin Mutun 13 ne akai jana'izar su Wanda wannan iftila'in yashafa a Daren jiya kamar yadda Ismael Bako Guga ya bayyana.
Lamarin tsaro dai a jihar Katsina yana ci gaba da zama barazana musamman a ƙananan hukumomin da lamarin yafi ƙamari, wasu bayanai da muka samu daga ƙaramar hukumar Faskari na cewa.
Yanzu haka mutanen garin Faskari da Unguwar Boka da Unguwar mai Sawa da Unguwar Gwanki da sauran garuruwa da suke Arewa da Faskari, kuɗi suke haɗawa za su kai ma 'yan bindiga a matsayin haraji don su bar su su yi noma Bana.
Wannan lamari na zuwa ne bayan da Gwamnati take bayyana irin ƙoƙarin da take yi wajen kawo ƙarshen ta'addanci a faɗin jihar Katsina, kodai cikin satin nan tawagar ƙungiyoyin matasa sun zagaya domin gane ma idon su irin wannan ƙoƙarin da Gwamnatin take yi. Ko a kwanannan an jiyo gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda yana bayyana cewa matsalar tsaro ta ragu da kaso saba'in cikin dari a jihar Katsina.