ZA MU FARA BIYAN MAFI ƘARANCIN ALBASHI NA N30,000 A WATAN YUNI, IN JI GWAMNAN ZAMFARA
- Katsina City News
- 23 May, 2024
- 454
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu Talatin a wata mai zuwa na Yuni.
Gwamnan ya yi wannan albashir ɗin ne a ranar Larabar nan a Lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa aiwatar da wannan mafi ƙarancin albashi ya nuna azamar gwamnatin jihar ne na kyautata jin daɗin ma'aikatan.
Sanarwar ta Idris ta ci gaba da ƙarin haske da cewa, gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu 30, maimakon Naira Dubu Bakwai da suke karɓa, za a fara biya daga watan Yunin nan mai zuwa.
A lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago ta NLC da na Malamai ta TUC, Gwamna Lawal ya bayyana cewa fara biyan wannan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu 30, wani yunƙuri ne na ƙara wa ma'aikatan Zamfara azama.
“A yau, ina so in sanar da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta jihar Zamfara cewa gwamnati na za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30 a watan Yuni.
“Tun lokacin da na hau kujerar gwamnan jihar Zamfara, gwamnati na ta aiwatar da sauye-sauye da dama na jin daɗin ma’aikatan gwamnati domin tabbatar da walwalar su.
“Mun samu nasarar biyan albashin ma’aikata na watanni uku da aka riƙe, biyan kuɗin hutu da sauran alawus-alawus.
“Gwamnati na ta biya jimillar Naira Biliyan 4,337,087,490 a rukuni huɗu ga waɗanda suka yi ritaya daga matakin jiha da ƙananan hukumomi, waɗanda ba a biya su haƙƙoƙin su ba tun shekarar 2011.
“Muna da wasu tsare-tsare na inganta ayyukan ma’aikatan gwamnati a Zamfara. Babu wani ma'aikaci da zai yi fargabar yin ritaya, saboda za mu tabbatar da biyan kuɗin ritaya a kan kari ba tare da wani jinkiri ba. Mun himmatu wajen aikin jin daɗin al'umma.”