Hukumar Hisbah a Katsina ta gabatar da Masu Laifuffuka Daban-daban a ranar Litinin
- Katsina City News
- 20 May, 2024
- 485
A wani samame da Hukumar ke yi don gyara da kauda Badala a jihar Katsina, Hisbah ta Katsina karkashin jagorancin Babban Kwamanda Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, sun gabatar da Masu Laifuffuka Daban-daban da aka kama a garin Katsina.
Wadanda aka kama sun hada da Mata Masu Zaman kansu, a wurare mabambanta na gidajen Badala, na bayyane da na Boye a garin Katsina, da Wasu Matasa da ake zargin su da satar kadarorin gwamnati, irinsu wayar lantarki, Kyabil da karafuna masu amfani da gwamnati take kafawa a titi don samar da hasken wutar lantarki da makamantansu.
Hukumar ta Hisbah ta ja hankalin Iyayen Yara da sauran al'umma akan kula da sa ido akan 'ya'yan su don taimakon kansu da gwamnati bisa wadannan bata gari akan cewa "su kiyaye duk wani abin Ash-sha da ka iya kaiwa ga hushin hukuma akansu."
Dakta Abu Ammar ya bayyana cewa "Ba nufin mu bane kamawa da kaiwa kotu don hukumta masu laifi a Katsina ba." Yace "Nufin mu a daina barnar ne, 'Ya'ya su zama jakadu na gari ga Iyayensu da Al'ummar da suke rayuwa a cikinta, kuma gwamnati tayi Alfahari dasu."
Yace "Amma bisa kin aikata daidai kuma duka wani ko wata bata gari da ta kuskura muka kamata akan bata Tarbiyya ko aikata ba daidai ba, lallai zasu fuskanci fushin hukuma."
An kama Masu laifin a wuraren da suka hada da Gabbi, da wasu boyayyun gidaje da hukumar ta samu rahoton yanda ake sheka aya a wuraren.
A wani labarin na daban hukumar ta zauna don sasantawa da kuma kawo gyara akan korafe-korafen Aure, don samun daidaito a tsakanin Ma'aurata, maida Aure tare da sasanta tsakanin Ma'auratan da Auren da ya riga ya kare da baya dauruwa, don samun kyakkyawar fahimta gujewa Ga-ba Musamman ga wadanda suka haifi zuri'a a tsakanin su.