Sarkin Gaya Zai Yi Bikin Naɗin Munzir Yusuf Ali sabon Sarkin Malamai ranar Juma’a
- Sulaiman Umar
- 11 May, 2024
- 386
Masarautar Gaya a Jihar Kano ta naxa Alhaji Munzir Yusuf Ali a matsayin sabon Sarkin Malamai Gaya.
An naxa shi ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa Sheikh (Dr) Yusuf Ali, fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya watanni shida da suka gabata, wanda shi ne mai riqe da sarautar kafin rasuwarsa.
Takardar naxin mai xauke da kwanan watan 8 ga Mayu, 2024 wadda Wamban Gaya, Alhaji Mansur Ibrahim Gaya ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai, na sanar da sabon Sarkin Malaman Gaya, Alhaji Munzir Yusuf Ali ranar da za a yi taron bikin naxa sa sarautar kamar yadda Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya ya umurta.
Sanarwar ta hakaito cewa za a yi bikin naxin ne a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu, 2024 da misalin qarfe 10 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya.
Masarautar ta kuma shawarci sabon Sarkin Malaman na Gaya da ya ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da nasarar naxin nasa tare da yi masa addu'ar fatan alheri da nufin Allah Ya yi masa jagoranci a wannan muqami.