Gwamnatin jihar Katsina ta raba Tallafi ga Iyalan Jami'an sa Kai (Yan Banga) da aka Kashe Naira Miliyan 20.
- Katsina City News
- 02 Sep, 2023
- 933
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Asabar 2 ga watan Satumba ne aka raba Tallafin ga Iyalan 'Yan Banga da suka rasa rayukansu da wadanda sukaji Raunika.
Tallafin ga Iyalan wadanda suka rasa rayukansu sun samu Naira dubu dari 5 ko wanne Iyali, su kuma wadanda suka samu rauni sun samu Tallafin Naira dubu 250.
Akwai wani jami'in Soja da ya rasa ransa a cikinsu wanda aka bayyana ranar da aka kasheshi ne aka haifar masa Ɗa, inda Iyalansa suka zo suka amshi Tallafin Naira Miliyan ɗaya 1 daga Gwamna Radd, sai wani Dansanda da ya samu rauni shima ya samu Tallafin.
Mai bawa Gwamnan Katsina shawara na musamman akan yanda za'a tallafawa wadanda hatsarin 'Yan Bindiga ya shafa, ya bayyana yanda tsarin tallafin yake da kuma ire-iren Ayyukan da Gwamnatin jihar Katsina take a karkashin Ofishinsa.
Gwamnan jihar Katsina ya bada Umarnin dik wanda wani Ibtila'i ya shafa na 'yan Bindiga tun daga jami'an tsaro zuwa mutanen gari, a karkashin ofishin Mataimakin na musamman akan yanda za a tallafawa wadanda harin 'yan Bindiga ya shafa, yace a kaisu asibiti ayi masu magani kyauata har sai sun warke. Yace "ya zuwa yanzu muna da Marasa lafiya a Asibitin koyarwa ta Gwamnatin tarayya a Katsina da kuma Asibitin Kashi," yace kuma cikin ikon Allah mafiya yawa sun warke an sallamesu.
Da yake tsokaci a madadin mai Martaba Sarkin Katsina Alh DR Abdulmumini Kabir Usman, wakilinsa Galadiman Katsina mai Shari'a Sadiq Abdullahi Mahuta, ya bayyana sakon sarki kai tsaye na nuna farin ciki da kuma godiya ga Gwamnatin jihar Katsina bisa wannan nuna damuwa da tayi akan wadannan bayin Allah. Sarkin Katsina ya bayyana cewa akwai shawara da zasu aikoma Gwamnati domin a kara dubawa. Sana ya bayyana goyon bayansa akan tsarin Kashe kudi ta fannin tsaro dari bisa dari, inda yace yana goyon baya dashi da hakimansa da magaddai baki daya. Mai shari'ar Sadiq Abdullahi Mahuta yace a madadin shi kansa a matsayinsa na Hakimin Malumfashi ya mika wata shawara akan jajirtaccen Dansandan nan Mutumin Dayi, inda ya bayyana gudumawar da Gwamnati mai wucewa ta Aminu Bello Masari ta bayar ta Naira Miliyan goma aga iyalansa yace saboda mutum ne mai yawan 'ya'ya yace an bada kudin domin kula da iyalansa da makarantar yaransa. Yace yana kira ga wannan gwamnati ta Dakta Dikko Umar Radda da ta sanya sunansa a ciki.
Sana ya bayyana cewa ko a jiya an kashe wani Danbanga a garin na Malumfashi, yana kira da a sake dubawa a shiri na gaba.
Da yake jawabi a madadin Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Radda, Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barasta Abdullahi Garba Faskari, yayi bani a madadin Gwamnan jihar Katsina inda ya bayyana Kudirori na Maigirma Gwamnan jihar Katsina, inda daga ciki yace yana daga cikin irin muhimmancin da Gwamnatin jihar Katsina ta dauki tsaro, cewa ta samar da wannan ofishin na musamman wanda yake sabo ne, yace ba don komai ba saidai don dubawa da kuma Tallafawa masu Ibtila'i na ƴanbindiga. Yace shiyasa aka samar da Ofishin mai bawa Gwamna shawara akan wadanda Ibtila'in 'Yanbindida ya shafa.
Sana kuma yace yana daga cikin damuwa da lamarin tsaro da gwamna yayi shine ya bayyana cewa zasu kashe fiye da naira biliyan 8 domin tabbatar da tsaro. Yace akan haka ake kuma farawa ake don kuwa mai girma gwamna ba zai taba samun kwanciyar hankali ba sai jihar Katsina ta samu zaman lafiya. Yace harkar tsaro ba ta jami'an tsaro kadai bace, ta kowa da kowa ce, yace bayan addu'a yakamata mutane su sanya ido sosai kuma su kai duk wani motsi da sukaji ko suka gani wanda basu gamsu dashi ba. Faskari yace akwai jami'an tsaro guda 20 da mutanen gari 86 da suke a Asibiti wanda Gwamnatin jihar Katsina ke daukar nauyin maganinsu, yace an sallami 46 saura 40. Yace sauran abin da zai biyo baya zakuji daga Maigirma Gwamnan jihar Katsina. A karshe yayi godiya ga ga jami'an tsaro da sauran al'umma, ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina Kofarta bude take akan Amsar shawara.
Da yake jawabi a wajen taron shugaban 'Yan Banga na jihar Katsina, ya bayyana cewa wadannan da za'a bawa tallafin ba wai na lokacin gwamnatin Dikko radda bane, jinkai da damuwa da lamarin ne ya sanya ya nemi a Tantance a kuma mika sunayensu domin samun tallafin, sana yace akwai wadanda aka kashe kwanannan wadanda ake cikin tattara bayanai kuma suma za'a bayyana abinda ya kamata a nan gaba. Daga cikin wadanda suka samu Tallafin akwai Haruna Rigoji, akwai iyalan Aminu Abubakar Helikwafta ada aka kashe, da da Mahara Barde, sauran sun hada da Muhammad Ragama Isa yar kabeluwa, da Abubakar Abdul'aziz. Akwai Alhaji Tsoho a Mahuta, da Salisu Adamu, Faruqu Halilu, a Safana, wanda kimanin Mutum 34 masu rauni da wadanda aka kashe.
Wadanda suka shedi shirin bayada Tallafin sun hada da dukkanin hakiman da abinda ya shafa a garin ko gundumarsu. Al'akalin alkalai na jihar Katsina, Girandi kadi, masu bawa Gwamna shawara da Kwamishinoni wasu daga cikinsu wakilan bangarorin tsaro da Kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, duk sun samu halartar.