'Yan bindiga a Kaduna sun bada wa'adin biyan Kudin Fansa ko a dibi gawarwaki
- Katsina City News
- 16 Mar, 2024
- 398
Yan Bindigan Kaduna Sun ba da wa'adin biyan kudin fansa naira biliyan ɗaya a cikin kwana 20, daga ranar da aka yi garkuwa da ɗaliban,
-Sun ce za su kashe su duka idan har ba a biya kuɗin fansar ba," kamar yadda mai magana da yawun iyayen yaran, Jubril Aminu ya shaida wa Reuters.
A ranar 7 ga watan Maris ne aka sace yara ƴan makarantar da ma wasu manyan ɗalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya.
Matsalar tsaro na ƙara ƙamari a arewacin Nijeriya musamman batun satar ɗalibai.
Ƴan bindiga da suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Nijeriya a makon da ya gabata, sun bukaci a ba su Naira biliyan ɗaya, kwatankwacin dala 620,432 a matsayin kuɗin fansa, kamar yadda kansilan yankin kuma mai magana da yawun iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A ranar 7 ga watan Maris ne aka sace yara ƴan makarantar da ma wasu manyan ɗalibai da kuma wasu ma’aikatan makarantar a garin Kuriga da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Nijeriya, a karon farko da aka yi garkuwa da mutane da dama irin haka tun shekara ta 2021.
Kansilan, Jubril Aminu, wanda kuma shi iyalan wadanda aka yi garkuwa da su suka zaɓa ya dinga magana a madadinsu, ya ce masu garkuwan sun kira shi ta wayar tarho ranar Talata.
“Sun buƙaci a biya su biya jimillar naira biliyan ɗaya a matsayin kudin fansa ga ɗaukacin ɗalibai da ma’aikatan makarantar,” in ji Aminu.
Yadda ƴan bindiga suka sace ɗalibai kusan 300 a wata makaranta a Kaduna
"Sun ba da wa'adin biyan kudin fansa cikin kwanaki 20, daga ranar da aka yi garkuwa da su, sun ce za su kashe dukkan ɗaliban da ma'aikata idan har ba a biya kuɗin fansar ba."
Shi ma Idris Ibrahim, wani zaɓaɓɓen jami’i a karamar hukumar Kuriga, ya tabbatar da batun bukatar kudin fansa da adadin kudin.
“E, masu garkuwa da mutane sun kira al’ummar ta lambar Jubril Aminu, suka kuma gabatar da bukatar,” in ji shi.
Ibrahim ya shaida wa Reuters cewa, "Sun kira ne daga wata ɓoyayyiyar lamba amma hukumomi na aiki don gano lambar."
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na daukar ƙwararan matakai domin ganin an sako daliban.
Reuters ya ruwaito cewa Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, bai amsa saƙon da ta aika masa ta son jin ta bakinsa ba game da buƙatar masu garkuwa da mutane.
Haka shi ma mai magana da yawun Shugaba Tinubu bai amsa buƙatar son jin ta bakinsa ba.
Sai dai, Ministan yada labaran kasar, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa, matsayar Tinubu kan sace-sacen da aka yi a Kuriga shi ne jami’an tsaro su tabbatar da sako mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da biyan masu garkuwa da mutanen ba.
"Shugaban kasa ya ba da umarnin cewa dole ne jami'an tsaro cikin gaggawa su tabbatar da cewa an dawo da wadannan yaran da duk wadanda aka yi garkuwa da su lafiya, sannan kuma su tabbatar ba a biya ko sisin kwabo domin kudin fansa ba."
Gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta kafa dokar hana biyan kudin fansa inda ta ce za a ɗaure duk wanda aka samu ya biya kudin fansa don a sako wani nasa.