Cikakken Bayani Game Da Gyaran Network Din Da Ya Shafi Bankuna, Kasuwancin Yanar Gizo A Nijeriya Da Kasashen Afrika Masu Yawa
- Katsina City News
- 16 Mar, 2024
- 466
MainOne shine babban kamfani mai samar da tsarin kebul na karkashin ruwa, ya bayyana cewa tsarin gyara na USB na karkashin teku na iya daukar tsawon makonni biyar kafin a kammala, kamar yadda kamfanin ya bayyana a jiya Jumma'a.
An samu matsalar ne bayan an yanke gabar tekun Afirka ta Yamma, dake tekun kasar Cote D'Ivoire, wadda take jone da Tekun Atlantika.
Katsewar ya yi mummunar tasiri, musamman ga bankunan Najeriya, saboda MainOne ya zama fitaccen kamfani mai samar da intanet ga wasu daga cikinsu, wanda sanadiyar hakan Bankuna da yawa ayyukansu suka tsaya suka kasa samun damar aikace-aikacen banki ko amfani da sabis na USSD da kuma harkokin hada-hadar kasuwancin Data da wasu kasuwancin yanar gizo, da kuma manyan kamfanoni da masana'antu da manyan hukumomin Gwamnati masu yawan gaske.
Kamfanin ya bayyana cewa tsarin gyaran wanda ya hada da jigilar jirgin ruwa don kwaso sassan kayan aikin da suka dace daga Turai da kuma hanyar wucewa zuwa Afirka ta Yamma, an kiyasta zai dauki kimanin makonni biyar kafin a kammala shi.
ME YASA MUKE DA NETWORK A NAJERIYA?
Bayan kebul din sun lalace akwai kasashen da Network dinsu kusan komai ya tsaya wasu kuma kadan ne ya tabu, amma mu namu na Najeriya ya tsaya a LOW ne, ma'ana muna da network din amma mai rauni wanda hakan yasa ake gudanar da al-amura sama-sama amma da zaran tsakar dare yayi komai yana tafiya da kyau saboda ana samun karancin masu amfani da Network din.
A yanzu haka kullum idan dare yayi Network yana da kyau sosai, a kusan lokacin ake cigaba da hada-hadar kasuwancin Data da sauran su.
Duk me bukatan siyan Data ta MTN da kyau ba tare da matsalar network ba, sai-dai ya dinga tashi da Dare zuwa safe, amma AIRTEL, GLO da 9Mobile a yanzu haka suna tafiya da kyau. Yawan da aka yiwa kamfanin MTN yasa aka fi samun karancin network na kamfanin.
Daga yanzu har zuwa lokacin da za a kammala gyaran, abubuwan da suka shafi yanar gizo da kasuwancin yanar gizo za su yita bawa mutanen Najeriya wahala bankuna da kasuwanci da yawa suna iya daskarewa wanda zai janyo a yi asarar biliyoyin kudade. Allah ya kyauta.
✍️ Comr Abba Sani Pantami
Marubuci, mai fashin baki, Mai bincike,
Dan jarida mai yada labarai a kafofin sada zumunta.