ƁARAYIN DAJI SUN KASHE JAMI'AN TSARON AL'UMMA BIYU A BATSARI
- Katsina City News
- 11 Mar, 2024
- 561
Misbahu Ahmad @ Katsina Times
Ɓarayin daji masu ta'ammuli da miyagun makamai, sun kashe jami'an tsaron al'umma waɗanda aka fi sani da Katsina community watch corps guda biyu a yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Wannan mummunan al'amari ya faru da misalin 12:50pm a ƙauyen Yasore dake cikin yankin na ƙaramar hukumar Batsari, a ranar lahadi 10-03-2024. Kamar yadda wasu daga cikin jami'an tsaron na al'umma suka shaida mana cewa "suna cikin sintiri a yankin na Yasore sai kawai ɓarayi suka mamaye su, kuma suka buɗe masu wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan jam'an biyu; Aminu da Ibrahim, sannan har yanzu akwai jami'i ɗaya da ba'a gani ba.
Anyi jana'zar waɗanda aka rasa kamar yadda makusantansu suka bayyana mana.
Hare-haren ƴan bindiga ga jami'an tsaro ba baƙon abu ba ne a yankin Batsari, domin a kwanakin baya ma sunkai ma jami'an tsaron ƴansandan kwantar da tarzoma harin kwanton ɓauna a ƙauyen sakijiki, inda suka kashe jam'in tsaro ɗaya.