HAUSAWA DA AL'ADARSU: Haɓaka Kasuwancin Kuɗi A Ƙasar Hausa
- Katsina City News
- 03 Mar, 2024
- 568
Daga: Shamsu Wapa Dandume
Hoton da aka ɗauka a shekarar 1964 a shahararriyar kasuwar ‘WAPA’ da ke Jihar Kano, a arewa maso yammacin Najeriya, ya nuna cewa canjin kuɗi, sana’ar Hausawa ce ta tsawon ƙarni.
Wapa, wacce aka kafa a matsayin cibiyar musayar kuɗi bayan yaƙin duniya na biyu, an ce an kafa ta ne a tsakanin 1946 zuwa 1948.
Asali, Wapa ta wuce kasuwar musayar kuɗi kawai. A gaskiya ma’anar ‘WAPA’ ta na nufin ƙungiyar Alhazai ta yammacin Afirka (West African Pilgrims Association), wadda ba ta da alaƙa da canjin kuɗi, sai dai babban wadda ya kafa ƙungiyar, Mamuda Ɗantata, ya zama dillalan kuɗi.
A farkon lokacin cinikin kuɗin Wapa, ma'amaloli sun haɗa da tsabar kuɗi. An jibge kuɗaɗen Najeriya a cikin buhunan Fam 100 (N 200), yayin da CFA Faransa 1,000 na CFA suke ajiye don musaya.
Haɓaka kasuwancin kuɗi a Wapa ya na da alaƙa da tarihinsa a matsayin wurin tsayawa ga ƴan kasuwa da matafiya daga Arewa da Yammacin Afirka, da mafarin mahajjata zuwa Saudi Arabiya.
A da dai, manyan mutane ne suka mamaye wannan sana’ar.
A tsarin al’adun Hausawa tsufa na da alaƙa da amana da kuma aminci.
Don haka, ana kyautata zaton duk wani dattijo wadda ya ke cikin wannan sana’ar, to lallai amintacce ne.
Sana'ar musayar kuɗi dai, wata sana'a ce da ta girku a nahiyar Afirka tsawon lokaci. Takan amfane fatake masu saye da sayarwa da tsabar kuɗi a yayin da suka ziyarci wata ƙasa domin kasuwanci.