Tsohon Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari Ya Kaddamar da Cibiyar Fasaha da Kasuwanci
- Katsina City News
- 25 Feb, 2024
- 385
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times.
A wani gagarumin taron da ya gudana a ranar 24 ga Fabrairu, 2024, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya kaddamar da cibiyar “Aminu Bello Masari Skills and Entrepreneurship Center” wanda Danlawan Katsina ya kafa. An gudanar da bikin ne a Lambun Danlawan, dake kofar Sauri a cikin birnin Katsina.
Cibiyar Wanda tsohon dan majalisar Tarayya daga karamar hukumar Katsina Hon. Hamisu Gambo, cibiyar tana da kyakkyawar manufa ta karfafa wa matasa sana’o’in dogaro da kai, da zummar bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban al’umma.
A yayin bude taron, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya bayyana jin dadin sa kan yadda Dan Lawan Katsina yake kokarin ci gaban al’umma. A ci gaba da nuna goyon baya, ya yi alkawarin bayar da gudunmowa na kansa don saukaka ci gaban koyar da sana’o’i a cibiyar.
Tsohon Gwamnan ya karkare jawabinsa da yin kira ga matasa da su rungumi sana’o’in hannu, tare da jaddada muhimmancin dogaro da kai a yanayin da duniya ke ciki a wannan zamani.
A nasa jawabin dan majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Hamisu Gambo ya jaddada kafa cibiyar domin ci gaban al’umma. Ya bayyana sauyin yanayi da kuma muhimmancin koyar da sana’o’in kasuwanci ga matasa, tare da samar da raguwar dogaro ga gwamnati.