Gwamna Dauda Lawal Ya Jagoranci Zaɓen Fidda Gwanin PDP Na Gwamnan Edo
- Katsina City News
- 23 Feb, 2024
- 516
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jagoranci zaɓen fitar da gwani na Jam'iyyar PDP a zaɓen Gwamnan jihar Edo da ke tafe.
A zaɓen da ya gudana yau Alhamis ɗin nan a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke garin Benin, Asue Ighodalo ne ya zama zakara, wanda ke nuni da cewa shi ne zai yi wa jam'iyyar takara a matakin Gwamnan jihar ta Edo.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Abuja, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, inda aka zaɓi wanda zai yi wa jam'iyyar PDP takara a zaɓen Gwamnan da ke tafe cikin watan Satumba mai zuwa.
Tun farko a jawabin sa kafin a fara zaɓen, Gwamna Dauda Lawal ya hori 'yan takarar da su yi amanna da tsarin zaɓen, inda ya ba su tabbacin za a gudanar da zaɓe mai cike da adalci.
“Ko yanzu za ku iya gani, an yi tsari mai kyau buɗaɗɗe. Za mu gudanar da zaɓe na gaskiya mai inganci don samar da ɗan takara ga jam'iyyar mu a jihar Edo."
Sanarwar ta Malam Idris ta ce, bayan kammala zaɓe da ƙirgawa, Gwamna Dauda Lawal, a matsayin sa na Baturen zaɓe, sai ya bayyana Ighodalo a matsayin gwanin da aka fitar. Inda Gwamnan ya bayyana cewa Ighodalo ya samu ƙuri'u 577, wanda ya doke sauran 'yan takarar su tara.
“A matsayi na na jagoran gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar PDP, na bayyana Asuelimen Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri'u 577.
“Ina taya shi murna, tare da yin kira ga sauran 'yan takarar da su karɓi wannan sakamako da zuciya ɗaya. Wajibin mu ne mu haɗa kai mu dumfari yaƙi na gaba, zaɓen Gwamna.
“Wajibin mu ne mu sanya buƙatun jam'iyya birbishin buƙatun mu. Yanzu muna da ɗan takara, dolen mu mu bayar da cikakken goyon bayan mu.