'YAN BINDIGA SUN KAI TAGWAYEN HARE-HARE A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 24 Jan, 2024
- 568
Ƴan bindiga sun kai tagwayen hare-hare a ƙauyukan Ƴanɗaka da Ɗan'alhaji dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Sun kai waɗannan jerin hare-hare a cikin daren ranar talata 23-01-2024, da misalin ƙarfe 08:30pm.
A Ƴanɗaka abun yayi muni, kuma sun nuna halin rashin tausayi da imani, domin kamar yadda wani da ya sha da ƙyar kuma mazaunin garin na Ƴanɗaka ya sheda ma wakilin mu, "muna zaune muna hira da abokai na, kawai sai muka ji an harba bindiga, kwa, sai nace lafiya kuwa? Kafin in rufe baki sai muka ji ko wace kusurwa an karɓa ana ta harbe-harbe kamar a filin yaƙi. Muka tashi kowa na gudun ceton rai domin kana gudu harsashi na wucewa ta gabanka, a haka har muka fita wajen gari wasu kuma suka maƙale cikin gidaje. sun kwashe fiye da awa ɗaya suna ta harbi kan mai'uwa da wabi. Da sun hango gungun mutane sai su bisu da gudu suna harbi, sai wanda Allah ya fidda. Sun kashe mutune biyu Malam Basiru wani dattijo mai kimanin shekaru 65 da wani yaro mai suna Haruna ɗan kimanin shekaru 12. Sun jikkata mutum ɗaya wanda tuni aka garzaya da shi asibiti domin yi masa magani"
sannan ƴan bindigar sun samu damar ɗaukar mutane ashirin, kamar yadda wani ɗan garin ya bayyana mana, daga ciki akwai mata 17 maza 3.
A Ɗan'alhaji kuwa wani ayari na ɓarayin dajin sun kai hari lokaci guda da na Ƴanɗaka, amma sun samu tirjiya daga mutanen gari, inda suka fito akayi ta ɗauki ba daɗi har ɓarayin suka fice daga ƙauyen ba tare da sun samu cikakkiyar nasara ba, sai dai sunyi awon gaba da wasu awaki ƙididdigaggu.
Shi dai wannan yankin na mazaɓar Ɗan'alhaji/Ƴangayya ya sha fama da irin waɗannan harehare na ƴan bindiga domin ko a ranar lahadi 21-01-2024 sai da suka kai irin wannan hari har suka sace mutane talatin wanda har ya zuwa wannan lokaci basu sako su ba.