TASHIN-TASHINAR ZARGIN KISAN JANAR ATTAHIRU: "An kama ni, an kulle ni, an kore ni don a toshe min baki" --Janar Ɗanjuma Keffi mai ritaya
- Katsina City News
- 24 Jan, 2024
- 484
Tsohon Kwamandan Rundunar Askarawan Najeriya Bataliya ta 1 da ke Kaduna, Ɗanjuma Ali-Keffi, ya bayyana yadda aka tsare shi kwanaki 64 saboda ya na zargin akwai wata ƙullalliya a hatsarin jirgin saman da ya kashe tsohon Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Attahiru.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar THISDAY a ranar Litinin, Ɗanjuma wanda ya ce an yi masa ritayar-dole saboda bai gamsu da yadda Attahiru ya mutu a hatsarin jirgi a Kaduna ba, ya rubuta wa Shugaba Bola Tinubu wasiƙa cewa a kafa wani sabon kwamitin bincike, domin binciken da aka yi lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, an binne shi a ƙasa, an ƙi fito da shi.
Yadda Aka Kama Ni, Aka Tsare Ni, Aka Yi Min Ritayar-dole’ -Ɗanjuma Keffi
Ya bayyana cewa an tsare shi kwanaki 64 a wani keɓantaccen wuri ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce a tsawon kwanaki 64 duk a ƙasa kan daɓe ya riƙa kwanciya, ba tabarma, ba karifa ballantana matashin-kai.
Ya ce kuma ya samu lalura ta rashin lafiya sakamakon waccan tsarewa da aka yi masa.
Cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, ya nemi a biya shi diyyar tsarewa da cire shi daga aikin soja ba bisa ƙa’ida ba.
Sannan kuma ya zargi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da yin biris kan halin da ya ke ciki, ballantana ya ceto shi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Janar Ɗanjuma Keffi ya ce akwai maƙarƙashiya a mutuwar Janar Attahiru, kuma ya yi kira ga Shugaba Tinubu ya yi bincike.
Tsohon Janar Mai Ritaya, kuma tsohon Kwamandan Askarawan Bataliyar Najeriya ta 1 da ke Kaduna (GOC), Ɗanjuma Ali-Keffi, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kafa kwamitin binciken gano musabbabin hatsarin jirgin saman Sojojin Najeriya, wanda ya kashe tsohon Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Ibrahim Attahiru.
Janar Ɗanjuma Keffi ya danganta haddasa haɗarin ga masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a ƙasar nan.
Ɗanjuma kuma ya rubuta wa Shugaba Tinubu ƙorafi dangane da abin da ya kira cewa, “an tsare shi ba bisa doka ba, an kama shi ba bisa doka ba, kuma an yi masa ritayar dole, saboda ana zargin ya fallasa fallasa asirin masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a cikin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.”
Cikin tattaunawar da Ɗanjuma Keffi ya yi da jaridar THISDAY a ranar Litinin, Ali-Keffi ya ce Janar Attahiru da wasu manyan sojoji 11 sun mutu a haɗarin jirgin sojoji wanda abin zargi ne, a ranar 21 ga Mayu, 2021 a Kaduna.
Janar Attahiru ya yi haɗari a Kaduna, lokacin da ya tafi domin halartar bikin yaye kuratan sojoji a Zariya.
Janar Keffi ya ce wancan binciken da aka yi, an binne shi a cikin rami, domin har yau ba a bayyana cikakken abin da aka gano jama’a sun ji ba.
Mutuwar Janar Attahiru: Allura Na Neman Tono Garma:
Ali-Keffi ya ce haɗarin da ya yi sanadiyar mutuwar Janar Attahiru abin dubawa ne. ‘Saboda ya mutu a daidai lokacin da ya ke kusa ga daƙile ta’addanci a Arewa maso Gabas, na Boko Haram.”
Ya ce daga cikin ƙoƙarin da Attahiru ya yi shi ne har da ƙoƙarin daƙile hanyoyin da ‘yan ta’adda ke samun kuɗaɗe da kuma makamai.
“Sannan kuma ya ya yi wa ƙulle-ƙullen ‘yan ta’adda ɗaurin-gwarmai, ta yadda har rikice-rikicen ya kaure tsakanin Ansaru da Boko Haram, wanda ya yi sanadiyyar kisan Shekau.”
“A ranar da su Janar Attahiru suka yi hatsari, an shirya ni ne zan tarbe shi.”
Ya ce abin mamaki sai duk aka canja wasu lokutan da aka tsara tun da farko.
An canja lokacin tashi, an canja jirgi, an canja wurin sauka kuma aka canja filin jirgin da za a sauka, daga filin saukar jirage na sojoji zuwa filin saukar jirage na Kaduna.
Lokacin saukar dai jirgin ya fuskanci yanayi maras kyau, sannan kuma sai aka ji wata irin fashewar ƙara mai toshe kunnuwa, kafin jirgin ya faɗo ƙasa.
Ya ce dukkan gawarwakin su Attahiru sun ƙone tun ma kafin jirgin ya faɗo. Wanda hakan na nufin wani abu ne ya fashe a cikin jirgin.
Ɗanjuma ya yi cikakken bayanin irin yadda suka riƙa aiki shi da Attahiru ta ƙarƙashin ƙasa wajen daƙile matsalar ta’addanci ba tare da an yayata ba.
“Kafin su Attahiru su taso cikin jirgi, na yi waya da shi, ya shaida min za su taso 1000hrs daidai washegari.
“Washegari ɗin da safe, 0630hrs, na kira Shugaban Ma’aikatan COAS ɗin, domin na ji idan lokacin tasowar na nan, domin na tsara wane masallaci zai je Sallar Juma’a.
“Amma sai COS ya ce min an canja lokacin tasowa. Ya ce min ai bayan mun gama waya da shi jiya, an kira shi an ce zai halarci taro, ko dai ofishin Ministan Tsaro ko kuma Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Juma’a ɗin, ƙarfe 1000 na safe, 21 ga Mayu, 2021. Kuma an je ya je da kan sa, kada ya tura wakilci.
“Kuma abin lura shi ne duk wani motsin da COAS zai yi wajen Abuja ko sauran Manyan Hafsoshin Tsaro, sai Ministan Tsaro da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa ya sani. Kuma sai Fadar Shugaban Ƙasa ta sani tun kafin lokacin fitar.
“Saboda haka, tunda an san Attahiru zai fita daga Abuja ranar Juma’a zuwa Kaduna da Zari’a, don me kuma za a kira shi wani taro a Abuja, a daidai lokacin da zai tashi zuwa Zaria? Kuma me ya sa aka je ya je da kan sa, kada ya tura wakilci?
“To ni dai ko a lokacin da aka ɗaga, ban san dalilin da ya sa aka ƙara ɓata lokacin awa ɗaya ba kuma kafin jirgin ya tashi 1730hrs.
Sai aka ce min wai wancan jirgin da ya kamata su hau ya na da ‘yar matsala, shi ya sa sai da aka yi canjin wani jirgin.”
Bayan sun gaji da jira, Ali Keffi ya faɗa a cikin tattaunawar yadda suka tafi filin jirgin Kaduna da kuma yadda jirgin ya faɗo a kan idon su, a daidai lokacin da suke shiga filin jirgi.
Ya ce sun ji wata irin ƙara kamar aradu ce ta faɗo, daga nan sai suka hangi jirgi na sulmiyowa ƙasa. Daga nesa kuma sai suka hangi wani ƙwallon jar wuta ya yi sama da ƙarfi. Ashe jirgin da ke ɗauke da Janar Attahiru ne!
Premium Times hausa