Ɗalibai shida 6 daga Makarantar Katsina State Institute of Technology and Management sun Sami Tallafin Karatu a Ƙasar Marocco
- Katsina City News
- 18 Jan, 2024
- 649
Zaharddeen Ishaq Abubakar Katsina Times
Makarantar ta Katsina State Institute of Technology and Management (KSITM) ta shirya taron bankwana ga daliban nata a ranar Alhamis 18 ga watan 1 na 2024 a Dakin taro na shugaban Makarantar.
Taron na bankwana ya kumashi Shugaban Makarantar Dr. Babangida Albaba, Malamai Dalibai da Iyayen Daliban gaba daya don yi masu Nasiha, Jan hankali da kara masu kwarin gwiwa akan abinda zasu je nema na Ilmi.
Dr. Babangida Abubakar Albaba (Rector) Shugaban Makarantar a jawabinsa ya taya Daliban Murna da yi masu bayani Daki-daki akan yanda tsarin yake da yanda zasu je da shekarun da zasu yi zuwa dawowa, inda yace yana alfahari da su a matsayin su na wadanda aka zaba su shida daga makarantar ta KSITM a cikin Mutum talatin da zasu tafi karatun a ƙasar Marocco daga Nijeriya.
Yace "Sannan Ku sani shi wannan Karatu Kyauta ne kuma kasar Marocco ta dauki nauyin su don kara dankon zumunci a tsakaninta da Nijeriya."
Da take tofa albarkacin bakinta shugabar Dakin Karatu ta Makarantar Hajiya Dr. Hindatu Salisu Abubakar ta bayyana jin dadin ta akan wannan Nasara da basu taba samu ba sai a wannan lokaci. Tace "Wannan abin farin ciki ne da murna yau ga Dalibai daga Makarantar mu ta KSITM ta yaye dalibai masu hazaka da zasu je ƙasar Marocco don yin Babbar Diploma." Tace sai mu godema Allah. Sana kuma ta bayyana wannan abin a bin murna ga Iyaye 'yan uwa da ma al'ummar jihar Katsina.
Dakta Hindatu ta ja hankalin Daliban da cewa su nema wa Makarantar da jihar Katsina dama Najeriya Mutumci a Idon Duniya duba da ba a ƙasar su suke ba duk abinda suka aikata na abin Ash-sha za a ce 'Yan Nijeriya ne, tace don haka su kiyaye.
Idris Tsaskiya shine ya gabatar da jawabi a madadin Iyayen Daliban, inda ya bayyana jin dadin su, yace "Wannan rana ta zama wata rana ta alfahari, da jin dadi maras misaltawa.
Sana ya jawo hankalin Daliban akan suyi amfani da shawarar da aka basu domin neman wa Iyaye, Makaranta, Jiharsu da Kasarsu Mutunci, kuma su dage da maida hankali akan abinda suka tafi koyo.