"Dubu Ashirin da biyu da dari biyar (₦22,500) muke ciyar da ko wane Fursuna a Nigeriya" Hukumar Kula da gidajen Gyaran Hali
- Katsina City News
- 05 Jan, 2024
- 501
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya ta yi watsi da wasu rahotanni dake yawo cewa ana ciyar da ko wane Fursuna a akan Naira dari biyu a rana, a maimakon ₦750 da gwamnatin tarayya ta kayyade.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Kwanturola Abubakar Umar, ya karyata ikirarin, yana mai bayyana haka a matsayin kazafi da rashin tabbatar da gaskiya.
Umar ya fayyace cewa fursunonin da ke gidajen yari a fadin kasar nan suna ciyar da su ne da kudi N750 da aka amince da su, kamar yadda gwamnatin tarayya ta kayyade.
Ya jaddada cewa tallafin ciyar da fursunonin bayanane yake a bainar jama'a ba wani abu bane da aka lullube.
Haka kuma, Umar ya amince da cewa su kansu kudin N750 da aka kayyade ana tattaunawa da neman hadin kai da gwamnatin tarayya don neman a sake fasalin alawus din ciyarwa don dacewa da yanayin tattalin arziki.
Sanarwar ta kuma jaddada nuna gaskiya a cikin tsarin saye da sayarwa, tare da bayyana kwangilar samar da kayan abinci a bainar jama’a, da kuma sharuddan da aka tanadar ga masu sha’awar kamar yadda dokar ta 2007 ta tanada. wadata, shiri, da rarraba abinci ga fursunoni a cikin kasafin da aka amince da shi.
A cikin shekarun da suka gabata, hukumomi sun nuna himma don inganta jin daɗin fursunoni, tare da haɗa ingantaccen tsarin gyarawa. A karshe sanarwar ta bukaci al’umma da su yi watsi da rahotannin karya tare da ba su tabbacin jajircewa da kwazo.
Haliru Nababa ya yaba matuka akan aikin kyautata rayuwar mutanen da ke tsare. Haka kuma Hukumar ta gyaran hali ta nuna jin dadin ta ga tallafin da ake ci gaba da samu daga ‘yan Najeriya masu kishin kasa.