SAMEER ISMAIL MUSAWA:BULAMAN KASAR HAUSA NA FARKO.
- Katsina City News
- 30 Dec, 2023
- 1005
Daga Suleiman umar @ Katsina Times
Mai Martaba sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar CON ya tabbatar da sarautar sameer Ismail musawa a matsayin sarautar Bulaman kasar Hausa na farko a tarihin kasar Hausa baki daya da tarihin masarautar Daura mai tsohon tarihi a duniya.
Wannan yana kumshe a wata takardar da mai
Martaba sarkin Daura ya rubuta ma Alhaji sameer Ismail musawa a ranar 29 ga watan disamba 2023 wadda sarkin na Daura ya sanya mata hannu da kansa kuma aka aika ma Alhaji sameer Ismail da wasikar ana tabbatar masa da bashi sarautar.
Sarkin Daura ya bayyana a cikin wasikar cewa,an ba Sameer wannan sarauta ne bayan tattaunawa da masarautar tayi ta tabbatar da irin taimakon da sameer ke bayarwa ga cigaban Katsina, da Kasar Najeriya da kuma taimakon al umma baki daya.
Takardar ta kara da cewa za ayi bukin nada ka a ranar da ka cimmawa tsakanin masarautar da kuma kai sabon bulama.ta cigaba da cewa sarkin Daura da masarautar na taya ka murnar wannan sarauta da Allah ya baka.
SARAUTAR BULAMA A KASAR HAUSA.
Bulama sarauta ce, mai daraja wadda take da tarihin sama da shekaru dubu a kasar Barno.abinda take nufi shine amintaccen shugaban al umma Wanda ya damu da cigaban su da kare rayuwarsu da bunkasar tattalin arzikin su.
Sarkin zaria marigayi Alhaji shehu Idris shine Wanda ya fara aro ta a kasar sarautar hausawa da fulani daga kasar barno Wanda a lokacin ya nada Alhaji shamsudden MD Yusuf bulaman farko.
Sarauta ce, mai tsohon tarihi wadda ba a baiwa kowa ita sai Wanda aka shaide shi da amana da kuma son cigaban al umma.
Mai martaba sarkin daura ya baiwa sameer ne, sarautar sakamakon abin da ya ji game dashi na taimakon al umma da son yan uwa da cigaban Katsina da Najeriya.
WANENE SAMEER ISMAIL MUSAWA?
Sameer Matashi ne a daga zuriyar sanyinawa da sullubawan musawa Wanda Allah yayi ma Nasibi tun yana karamin yaro,mukamin da ya fara rikewa tun kafin ya kai shekaru ashirin shine mai taimakawa Marigayi Badamasi kabir Usman ( Allah ya jikan shi da Rahama) Marigayi Badamasi ya rike sakataren masarautar Katsina na tsawon shekaru ya kuma zama zabbabben Dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta tafiya. Daga mukaman da ya rike sune.
Ya rike mukamin bod memba a hukumar REB a jahar Katsina ya rike mukamin daya daga cikin Kwamitin zaben Tinubu daga arewacin Najeriya.
Yanzu yana rike da maitamaka ma shugaban majalisar dattawan Najeriya na musamman daga arewacin Najeriya.
Sameer da kasuwa ne da yake da kamfanoni daban daban daga cikin su akwai kamfanin noma da sarrafa kayan noma na Sameer Agro alied Ltd, da kamfanin Sameer table water da kuma kamfanin shi na harkokin mai da iskar gas.
An baiwa sameer mukaman girmamawa da yawa daga cikin su akwai ambassador na majalisar dinkin duniya,an kuma bashi digrin girmamawa, kungiyoyi sama da Saba in sun karrama shi.
Sameer yana da Mahaifiyar sa a raye mai suna Hajiya Murnajatu Ismael musawa da kuma mata guda uku hajiya Niima hajiya Amina da Hajiya zainab sameer Ismail da ya ya takwas
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779.08057777762