GARIN KUSADA, DA ASALIN SARAUTAR BEBEJIN KATSINA.
- Katsina City News
- 09 Dec, 2023
- 984
Garin KUSADA Yana kan hanyar Katsina zuwa Kano, amma ya dan shiga lungu kadan kusa da Gidan mutum daya. Kusada a halin yanzu, Karamar Hukuma ce mai zaman kanta, wadda aka cira daga Karamar hukumar Kankia.
Tarihi ya nuna an kafa Garin KUSADA tun lokacin Sarakunan Habe. A sabili da haduwar wasu Malamai da suka fito daga bangaren Kano, wasu Kuma daga Katsina suka hadu kusa da wata babbar korama suka zauna amma kowa da bangaren shi. Suna KUSADA ya samo asaline daga kwatancen da Mutane suka rikayi idan zasuje Garin watau, zamuje wancan Dan Garin Kusa da Kano, to daganan Sai aka takaita zuwa KUSADA.
Bayan da wannan wuri ya kafun Sai aka yi ta samun jama'a daga sassa daban- daban na kusa dana nesa suna matsowa, suna Kara wa wurin yawa, har gari ya bunkasa. Babban abinda ya Kara wa Garin jamaa shine wurine Mai dausayi da wurin kiwo Wanda ya jawo hankalin Fulani da sauran makiyaya zuwa wannan wuri. Haka Kuma zaman wannan Gari a kan hanyar zuwa Kano ya Kara Masa kwararowar Baki da Yan Kasuwa da sauran masu Sanaa ta gargajiya kamar Kira da saka da rini da sassaka da sauransu. Ta hakane Kuma Garin ya shahara bisa hada Hadar Kasuwanci.
Hakanan Kuma wata ruwayar ta nuna cewa mutanen farko da suka zo, suka zauna kusada sun fitone daga Buntusu wadda ke yankin Roni ta Kasar Jigawa. Wasu Kuma sunce sun fitone daga Garin Yandadi Wanda ke cikin yankin Yashe ta Kasar Kankia.
Dangane da masu Sarautar Hakimcin Kasar Kusada Abinda zaa tunawa, wasu daga cikin zuruar Dallazawa sunyi Hakimin Kusada fiye da shekara Dari da Hamsin da suka wuce. To dagananne Sai Hakimcin ya mutu a garin. Ba a sake samun wani Hakimi ba Sai a shekarar 1992 Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman ya nada Alhaji Nuhu yashe a Matsayin Hakimin Kusada.
Daga cikin Dagattan Kusada akwai.
1. Galadima Bala.
2. Galadima Kado shekare
3. Galadima Abdulkarir
4. Galadima Mani
5. Galadima Ibrahim 1992 a matsayin Dagaci.
Bebejin Katsina Alhaji Nuhu yashe a matsayin Hakimi 1992 zuwa yanzu.
ASALIN SARAUTAR BEBEJIN KATSINA
Kamar yadda Yadda Tarihi ya nuna ita wannan Sarautar ta Bebejin Katsina an faratane a lokacin Dallazawa, Kuma a wancan lokacin ba tana a matsayin Hakimi babe, tana da rawar da take takawa a Masarautar Katsina.
Mutum na farko da aka Fara nadawa Bebejin Katsina shine Bebeji Gidado Wanda Sarkin Katsina Ummarun Dallaje ya nadashi a shekarar 1809.
Aikin Bebejin Katsina shine Kula da Shanun da gaba dayan Shanun dake Kasar Katsina , sannan Kuma Yana daga cikin manyan masu ba Sarki Shawara akan abinda ya shafi Fulani Makiyaya da Manoma.
Ga jerin sunayen wadanda sukayi Sarautar Bebejin Katsina daga cikin Zuruar Dallazawa.
1. Bebeji Gidado
2. Bebeji Bawa
3. Bebeji Tukur.
4. Bebeji Bello.
5. Bebeji Yusuf Abubakar dan Sarkin Katsina
Abubakar , shine mahaifin Mariganyi Ummaru Lafiya uwar jiki da Mariganyi Mamman D. O
Dallazawa sunta wannan Sarauta har tsawon shekara Dari da Hamsin 1809-1960. Tun daga wannan lokacinne baa sake nada kowa wannan Sarauta ba, Sai a shekarar 1975, Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ya nada Alhaji Nuhu Yashe wannan Sarauta ta Bebeji, lokacin yana Sakataren Majalissar Sarki.
Inda daga bisani acikin shekarar 1992 da aka Kara gundumomi aka cire Kusada daga Kankia itama aka bata Hakimci.
A lokacin ne Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammad Kabir ya tabbatarma da Alhaji Nuhu Yashe Hakimin Kusada Kuma ya zauna a matsayin shi na Bebejin Katsina. Abin lura anan shine Alhaji Nuhu Yashe an nadashi Sarautar Bebejin tun lokacin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo, Amma Bai zama Hakimin Kusada ba Sai cikin shekarar 1992, watau lokacin Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammad Kabir.
A halin yanzu Kasar Kusada tana da Magaddai guda (13) kamar haka:--
1. Magaji Magam
2. Magaji Yashe
3. Magaji Bauranya
4. Magaji Kafarda
5. Magaji Kusada
6. Magaji Mawashi
7. Magaji Aganta
8. Magaji Dudunni
9. Magaji Boko
10. Magaji Kaikai
11. Magaji Dangamau
12. Magaji Kofa
13. Magaji Tufani
Alhaji Musa Gambo Kofar soro