An kaddamar da tsige shinkafa a gonar dadin Kowa dake karamar hukumar funtua
- Sulaiman Umar
- 04 Nov, 2023
- 1223
Kamar ko wace shekara, a wannan karon ma Gimbiya 'yar sarkin noman Funtua, Garba Dan Ammani ta kaddamar da bikin tsige shinkafa a gonar na ta wacce aka fi sani da "Dadin Kowa Farm" da ke karamar hukumar Funtua a garin Dakamawa.
A yayin bikin tsige shinkafar, Gimbiyar ta yi jawabi a inda ta fara da cewa: " Da farko dai ina mika godiya ta musamman ga Allah madaukakin sarki da ya kawo mu wannan lokacin, hakika daminar bana tayi albarka domin ko mun ga amfanin gona kwarai da gaske, munyi shukokinmu lafiya gashi Kuma zamu fara girbe abinda muka shuka"