Gwamnatin Buhari ne Ta Haifar da Kalubalen Tattalin Arziki da ake Fuskanta A Halin Yanzu
- Katsina City News
- 13 Nov, 2023
- 747
Mai Baiwa Shugaban ƙasa Shawara kan Harƙoƙin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu ya Amince da kalubalen kuɗi da Gwamnati mai ci ke fuskanta a ƙarƙashin Jagorancin Shugaba Bola Tinubu. Ya danganta matsalar tattalin arzikin da ake fama da shi a halin Yanzu Ga Gwamnatin Tsohon Shugaban ƙasa Buhari da suka Gada daga Gwamnatin da ta shuɗe.
Duk da irin waɗannan Matsalolin, Nuhu Ribadu ya Tabbatar wa da Rundunar tsaron Kasar nan a kan jajircewar Gwamnati na Tabbatar da ingantacciyar kulawa da na'urorin tsaro. Ya kuma jaddada Aniyar Gwamnatin na cika ka’idojin Rundunar soji, Duk da Cewa ana fuskantar matsi na kasafin Kuɗi.
KBC Hausa News